For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

BABBAN TARON APC: Mutane Da Yawa Sun Sami Raunuka Lokacin Da Ƴansanda Suka Sa Tiyagas

Wakilai da kuma magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun sha hayaki mai sanya hawaye (teargass) yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin samar da nutsuwa a ƙofar shiga filin taro na Eagle Square da ke Abuja, inda jam’iyyar APC ke gudanar da Babban Taron Zaɓen Shugabanninta na Kasa.

Mutane da dama sun sami raunuka a cikin yamutsin.

Kofofi biyu da ake da su a filin Eagle Square da suka haɗa da wadda ta biyo ta ofishin Head of Service da kuma ta wajen ajjiye motoci na Federal Secretariat sun cika maƙil da magoya baya da kuma wakilai waɗanda suke ƙoƙarin shiga filin taron.

A hanyar ta bangaren ofishin Head of Service, taron mutanen ya fi ƙarfin jami’an tsaron da aka saka, inda mutane suka bude kofar wanwal suka dinga shiga, ciki har da waɗanda ba a tantance ba.

Ƴansanda sun yi amfani da hayaƙi mai sanya hawaye, kafin su samu nasarar shawo kan matsalar tare da rufe ƙofar, inda suke barin iya waɗanda aka tantance suna shiga.

(THE NATION)

Comments
Loading...