For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

BABBAN TARON PDP: Babu Abin Da Zai Kai Ni In Zauna Cikin Haramtattun Shuwagabanni – Aminu Ringim

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Jigawa a jam’iyyar PDP, Malam Aminu Ibrahim Ringim, ya bayyana dalilin sa na kauracewa rumfar jihar Jigawa yayin Babban Taron jam’iyyar PDP na kasa a satin da ya gabata.

Aminu Ringim ya bayyana hakan ne ga taron matasa magoya bayansa da suka ziyarce shi a mahaifarsa, Ringim, musamman domin yi masa bangajiya game da zuwa Babban Taron PDP na Kasa da kuma taya shi murnar nasarar taron da a cewarsu su suka samu.

Da yake jawabi ga matasan, Aminu Ringim ya ce “babu abin da zai kai ni in zauna cikin haramtattun shuwagabanni, domin kowa ya sani a jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ba a yi zaben mazabu ba, ba a yi zaben shugabannin kananun hukumomi ba ballantana ma Jiha, kowa ya sani. Kuma wannan matsala tana gaban kotu muna sauraren hukunci. Ta yaya kuma zan je cikin haramtattun shuwagabanni in zauna, kenan ma na yadda da su ko?

“Wannan shine asalin dalilin da ya hana ni zuwa rumfar jihar Jigawa domin a shekarun baya da muke da ingantattun shuwagabannin jam’iyyar ai ina zuwa.”

Aminu Ringim ya kara da cewa, “ko gobe idan an yi gyara an fitarwa da jam’iyyar PDP Reshen jihar Jigawa shugabanci mai tsafta da inganci to Insha Allahu da mu za a yi komai.”

An ta samun maganganu da tambayoyi kan rashin ganin tsohon dan takarar gwamnan da magoya bayansa a rumfar jihar Jigawa a wajen Babban Taron PDP.

Sai dai kuma an gano Aminu Ringim din cikin tawagar ‘yan PDP na jihar Kano bangaren tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso.

An raba gari tsakanin tsohon dan takarar gwamnan ne bayan faduwa zaben shekarar 2019, abin da dan takarar ya zarga a matsayin yi masa makarkashiya daga bangaren tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

Wannan ta sanya Aminu Ringim da magoya bayansa jan daga da tsohon gwamnan, inda suka nuna rashin amincewa da zabukan shugabancin jam’iyyar a jihar, bisa zargin tsohon gwamnan da yin danniya don cimma manufarsa ta kawo dansa a matsayin dan takarar gwamna a zabe mai zuwa.

Sai dai kuma, bayan rantsar da shi, sabon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Jigawa Babandi Ibrahim Gumel, ya bayyana cewa, zai yi iya mai yiwuwa wajen ganin an sasanta da duk wadanda aka samu sabani da su a jam’iyyar domin samun nasara.

Comments
Loading...