Alamu a ranar Lahadin da ta gabata na nuni da cewa a jihohin da aka gudanar da babban zaben All Progressives Congress (APC) kuma aka sami rarrabuwar kai, Jam’iyyar za ta amince da wadanda gwamnonin APC ke marawa baya.
Wani dan jam’iyyar kuma memba a babban taron jam’iyyar na kasa, wanda ya shaida wa daya daga cikin wakilan PUNCH, ya ce a jihohin da APC ba ta da gwamna, jam’iyyar za ta amince da wadanda manya masu rike da mukaman siyasa suka amince da su.
Bayanai na nuni da cewa, idan matsayin jam’iyyar ya tabbata, jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da Sanata Ibikunle Amosun, da Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbeola, da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, da Sanata Ibrahim Shekarau, da Sanata Barau Jibril na iya rasa nasara a rikicin mukaman jam’iyyar da ake a jihohinsu.
Tashe-tashen hankula da zanga-zanga sun rikita babban taron zaben shugabannin APC na jihohi da aka gudanar a duk fadin kasar a ranar Asabar inda rarrabuwa ta samu a jihohin da suka hada da Legas, Ogun, Kwara, Osun da Kano.
A jihar Ogun, wani bangare mai biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Sanata Amosun, wanda ya gudanar da babban taron sa a fadar Alake na Egbaland, ya zabi Cif Derin Adebiyi a matsayin shugaba.
Amma wani bangaren da ke goyon bayan Gwamna mai ci, Yarima Dapo Abiodun, ya gudanar da babban taron sa a filin wasa na MKO Abiola, inda Cif Yemi Sanusi, ya zama shugaba.
A jihar Kano, yayin da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje suka zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, yayin da wani bangare mai adawa da bangaren gwamna karkashin Sanata Ibrahim Shekarau ya zabi Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.
Taron zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihar Legas, wanda aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena, ya samu halartar Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Cornelius Ojelade ne ya fito a matsayin shugaban jam’iyyar daga bangaren masu ruwa da tsaki, yayin da abokin adawarsa, daga bangaren Lagos4Lagos, ya zabi Sunday Ajayi daga Karamar Hukumar Agege a Hotel Airport Ikeja, don jagorantar jam’iyyar.
A jihar Osun kuma, kungiyoyi masu biyayya ga gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola da wanda ya gada, Aregbesola sun gudanar da mabanbantan taron zabar shugabannin jam’iyyar.
A jihar Kwara, kungiyoyi masu biyayya ga Gwamna jihar, AbdulRahman AbdulRazaq da masu biyayya ga Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed suma sun zabi shugabanni daban -daban.
A ranar Lahadin da ta gabata, jaridar PUNCH ta gano a Abuja cewa, bisa ga al’adarta, APC za ta mutunta ra’ayoyin gwamnoni a jihohin da jam’iyyar ke da gwamnonin, sai kuma jihohin da ba ta gwamnioni a nan kuma za ta mutunta manyan masu rike da mukaman siyasa.
Wani memba na kwamitin jam’iyyar na kasa, wanda ya zanta da daya daga cikin wakilan PUNCH kan bukatar a boye sunansa, ya ce “don kada a samu cikas ga kokarin samun sulhu.”
Ya kara da cewa, “Me yasa tsohon gwamna zai so ya kalubalanci gwamna mai ci wanda duk mun san shine shugaban jam’iyyar a jihar? Dabi’a ce ta girmama gwamnonin mu masu dama a cikin irin wadannan al’amura.”
Wannan, na zuwa ne a matsayin mayar da martani kan kararrakin da aka shigar kan babban taron jihohin daga jihohin Ogun, Kwara, Enugu, Kano da sauransu.
Bayan jihohin da APC ke iko da su, akwai kuma wasu jihohin da jam’iyyar ba ta da gwamna.
Misali, a jihar Enugu, tsohon Kwamishinan Ayyuka, Mista Ugochukwu Agballah da wani tsohon Shugaban Jam’iyyar, Adolphus Udeh, sun fito a matsayin shugabanni a babban taron zaben gwamnoni da aka gudanar ranar Asabar.
A jihar Sakkwato ma an samu bangarori biyu da suka bullo inda aka gudanar da taro daya a sakatariyar jam’iyyar na jihar, wanda ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Tsakiya, Aliyu Wamakko; Sanata Ibrahim Gobir, Ministan Harkokin ‘Yan sanda, Maigari Dingyadi, tsohon Ministan Sufuri, Yusuf Suleiman, da sauransu wadanda suka zabi Isa Sadiq Acida a matsayin shugaba.
Yayin da kuma a wani bangaren karkashin jagorancin dan majalisar tarayya mai wa’adi uku Abdullahi Balarabe Silame, ya gabatar da Muhammad Daji a matsayin shugaba.