Shugaban matasan jam’iyyar PDP na ƙasa, Mohammed Kadade Sulaiman yace duk wani yunkuri na haɗa ƙarbuwar siyasar marigayi Moshood Kashimawo Abiola da ɗan takarar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace babban zunubine a siyasa.
Yayin da yake amsa tambayoyin yan Jarida a a Kaduna bayan kaddamar da wata ƙungiyar da zata taimakawa Atiku yaƙin neman zaɓe a gaban manyan shuwagabannin jamiyyar na Arewa maso Yamma, Suleiman ya ce “Tinubu yana tare da yan siyasar da suke kan mulkine amma bai karbu a wajen masu zabe ba”.
Ya ce duk wanda yake ƙoƙarin haɗa Tinubu da Abiola to tabbas ya aikata babban zunubi, saboda Abiola sananne ne a kowanne lungu da saƙo na ƙasar nan “kamar Atiku”, in ji shi.
Duk da haka, shugaban matasan ya tabbatar da cewa, jam’iyyar PDP za ta kayar da APC duk da suna kan mulki.
“PDP zata yi nasara a kan APC a babban zaɓen 2023 saboda abubuwa da yawa sun canza daga 2015 zuwa yanzu. Sunyi alƙawarin samar da tsaro, wutar lantarki, ilimi da sauransu, kuma a ƙarshe sun gaza cikawa sun kasa kare rayuka da dukiyar mutane, wannan lokacin, kowa ya ga yanda siyasa take tafiya, jama’a suna tare da PDP.
“PDP bata tsoron APC duk da tana kan mulki domin muna kan mulki muka fadi a 2015. Wannan lokacin mun shirya tsaf domin dawowa kan mulki. Bama tsoron gwamnati. Gwamnatin APC ta yi alkawarin gudanar da sahihi kuma nagartaccen zaɓe.”
Kadade ya kara da cewa, “Duk masu haɗa Tinubu da Abiola suna aikata babban zunubi a siyasa. Idan ka je Zariya akwai gidan da ake kira gidan Abiola, amma Tinubu kawai yana tare ne da mutanen da suke kan mulki, masu zaɓe basa tare da shi” in ji Kadade.
Da yake magana akan yanda yan ta’adda suke kaiwa hari yayin gangamin yaƙin neman zaɓe ya ce, “Bama tare da siyasar jagaliyanci tsakanin matasa, kullum muna basu shawara su guji bangar siyasa, muna kira garesu da duk wanda ya ce su sari wani ko su ci mutuncin wani su ce masa ya sa ɗan sa. Duk wanda suke amfani da yan daba basa kaunar damukuradiyya.”
Shugaban na matasa ya yi tsokaci a kan takarar shugaban ƙasa ta ‘yan addini ɗaya’ da APC ta tsaida, ya ce yan Arewa ba zasu amince da takarar Musulmi da Musulmi ba, wanda suke amfani da addini dan samun nasara a zaɓe, ya kamata su sani ba zata yi aiki ba wannan karon. Yan Najeriya suna san wanda yake ƙwararre ne kuma zai haɗa kan ƙasar nan.