Babbar Kotun Jihar Jigawa mai Lamba 6 da ke zamanta a Birnin Kudu, karkashin Alkali Musa Ubale, a yau Laraba, ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutane hudu, Umar Danladi, Abdussalam Sale, Auwalu Yunusa da kuma Mu’azu Abdurrahman a kan samunsu da laifin aikata fyade.
Daya daga cikin wadanda akaiwa hukuncin, Umar Danladi dan asalin Sabuwar Gwaram a Karamar Hukumar Gwaram da ke jihar, an kama shi ne da laifin yaudara da kuma tilasta dalibar firamare ‘yar shekara 8 da yi mata fyade a hanyarta ta dawowa daga makaranta.
Shi kuma mai laifi na biyu, Abdussalam Sale dan asalin kauyen Rafawa da ke Karamar Hukumar Dutse a jihar an kama shi da laifin yiwa yarinya ‘yar shekara 12 fyade wadda ya hadu da ita a tsakanin Sabon Garin Barnawa da kauyen Kishin Gishin Gawa, laifin da a farko ya amsa amma daga baya ya musanta.
Shi kuma Auwalu Yunusa wanda dan asalin garin Kafin Fulani ne a Karamar Hukumar Gwaram an kama shi da laifin yiwa yarinya ‘yar shekara 6 fyade bayan ta dawo daga aiken da yai mata.
Na karshen cikin masu laifin, Mu’azu Abdulrahman wanda ya fito shima daga Sabuwar Gwaram a Karamar Hukumar Gwaram, an kama shi da laifin yaudarar yarinya ‘yar shekara 8 tare da yi mata fyade a wata gonar dawa yayin da take dawowa daga makaranta.
Jami’ar Hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Shari’a a Jigawa, Zainab Baba Santali, ta bayyana cewa, bayan tabbatar da laifuffukan mutane hudun, Alkali Musa Ubale ya yanke musu hukuncin daurin rai darai, kamar yanda Sashi na 283 na Kudin Manyan Laifuffuka na Jigawa ya tanadar.