For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Babu Dan APC Da Zai Bigi Kirji Ya Ce Sun Sauke Nauyin Da Suka Dauka – Danjani Hadejia

Daga: Abubakar Tahir Hadejia

Mai taimakawa na musamman ga Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana takaicinsa kan halin da kasar nan ke ciki a yanzu.

Jigo a jam’iyyar hamayya ta PDP ya bayyana cewa, bai kamata su zuba ido suna kallon cin kare ba babbaka da akeyi da rayukan al’ummar da suka yi ruwan kuri’u ga jam’iyya mai ci ta APC ba.

Danjani ya bayyana cewa a yanzu babu wani dan jam’iyyar APC da zai bigi kirji ya nuna sun sauke nauyin da suka dauka na samarwa kasarsu tsaro.

“Abin takaicin shine, kisan da ake yiwa al’ummar Arewacin Kasarnan duk da hannun shuwagabannin dumu-dumu,” in ji Danjani.

Umar Danjani ya nuna alhininsa kan yanda wasu kungiyoyin addini wadanda suka rinka caccakar jam’iyyarsu a baya kan rashin tsaro, amma yanzu sunyi gum da bakinsu.

Danjani ya bayyana cewa irin wadannan kungiyoyin addinin ba su da banbanci da na siyasa, kuma hakan ya tabbatar ba sa kishin kasarsu.

Ya kara da cewa babu yadda za a yi su zuba ido suna kallo wannan halin da ake ciki, saboda haka dole ne su fito su bayyanawa Shugaba Buhari Gaskiya.

Danjani ya kara da cewa kamata yai a ce ya zuwa yanzu, ‘yan Nigeria sun sha romon demokaraɗiyya da suke fatan samu amma wannan gwamnatin ta gaza.

Danjani ya bayyana cewa jam’iyyar PDP tana cikin damuwa ganin yadda kasar kullum ke komawa baya.

Daga karshe jigon a PDP ya yi kira ga ‘yan Nigeria da su fara shirye-shiryen zabe mai gabatowa, su yiwa jam’iyyarsu ruwan ƙuri’u, domin samarwa kasar nan cigaba mai dorewa.

Comments
Loading...