For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Babu Tabbacin Yin Babban Taron APC A Fabarairu, Kwamitin Sasanto Sun Bukaci Karin Lokaci

Tababar data dabaibaye jam’iyyar APC mai Mulki a Najeriya, duk da fadi tashin da kwamatin sulhunta tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar keyi na daidaita Tsakani, yaci tura a wasu jihohin.

Abinda ake ganin zai iya haifar da koma baya, koma ya sanya dakatar da gangamin jam’iyyar na kasa data shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan faburairun nan.

Kwamatin sulhun da aka kirkira a ranar 15 ga watan Satumbar Bara karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, a ranar litinin din nan ya sake neman Karin sati guda, don kammala sauraron korafe-korafen da fusatattun ‘yan jam’iyyar suka shigar gaba gare shi.

Saidai a zantawarsa da wakilin mu, wani gwamna a jam’iyyar ya shaida cewa shi da ire-irensa suna kan bakan su, na kin goyon bayan dage gangamin da jam’iyyar ta tsara gudanarwa a karshen watan Faburairun nan,

Duk kuwa da buqatar da kwamatin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar suka miqawa kwamatin shirya wannan gangami na neman Karin wa’adin mako daya, don kammala aikinsa na hade kan ‘yan jam’iyyar.

Ana hasashen kwamatin ta Abdullahi Adamu ya bi diddigin rikice-rikice tsakanin ‘yan  jam’iyyar tun daga matakin Mazabu, zuwa kananan hukumomi da jihohi a fadin kasar nan.

Bisa ga jadawalin da jam’iyyar ta APC ta fitar, kwamatin sulhun zai gabatar da rahoton sa a ranar litinin, abinda zai baiwa jam’iyyar damar fitar da masu ruwa da tsaki na babban taron jam’iyyar a ranar Alhamis din mako na Uku na wannan wata.

daga ranar 14 ga watan Faburairu ne jam’iyyar zata bude sayar da takardar neman tsayawa Takara a matakai daban-daban na jam’iyyar a kasa,

za’a rufe karbar form din, bayan kamala cikewa kafin ranar 19, ga watan faburairun 2022.

Aikin tantance ‘yan takarkarun shugabancin jam’iyyar, dake zawarcin maqamai a matakin kasa, zai kasance tsakanin ranakun 20 zuwa 22 ga watan faburairun.

Sai kuma, Karkare tantance Dalagets a ranakun 24 zuwa 25 ga watan faburairun 2022, gabanin shiga gangamin ranar 26 ga wata.

A jawabin sa, gwamnan Yobe kuma shugaban kwamatin riqo na jam’iyyar APC na kasa Maimala Buni, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan Nasarar jam’iyyar a zabubbukan dake tafe.

Comments
Loading...