For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Badaru Ya Ce Kananan Yara Na Batan Dabo A Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, a ranar Alhamis ya yi kira ga iyaye da al’umma da idan sun ga bakuwar fuska a yankunansu, su gaugauta sanar da hukumomi.

Badaru yayi kiran ne bayan samun rahotanni da suke nuni da cewa ana samun batan dabon kananan yara a jihar a ‘yan kwanakin nan.

Mai magana da yawun gwamna Badaru, Habibu Nuhu Kila ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Ya ce gwamnan yayi kira ga iyaye da sauran jama’a da su farga, kuma su sa wa ya’yansu idanu wajen sanin zirgazirgar su don kar su fada hannun mugaye.

Sanarwar gwamnatin ba ta bayyana yawan yaran da ake nema ba, amma binciken wakilin PRIMIUM TIMES ya gano cewa a kalla yara biyar sun bata a cikin makonnin da suka gabata a fadin Jihar.

Kakakin hukumar ‘yan sandan Jigawa, Lawan Shiisu, ya tabbatar da lamarin bace-bacen yaran, yayin da hukumar ‘yan sandan na tattara alkaluman yawan adadin yaran da suka bace zuwa yanzu.

Badaru yace gwannati a tsaye take kan tabbatar da tsaro a jihar, kuma ta dukufa wajen samar da walwalar al’ummarta, kuma za ta cigaba da samar da tsaro a fadin Jihar.

Gwamna Badaru yayi kira ga al’umma da masu ruwa da tsaki su tashi su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Jihar.

Comments
Loading...