Daga: Kabiru Zubairu
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2022 ga majalissar dokokin jihar a yau Laraba.
Gwamnan ya bayyana cewa a shekarar 2022 gwamnati za ta kashe kudi Naira Biliyan Dari da Saba’in da Bakwai da Miliyan Dari Bakwai da Casa’in da Biyar da Dubu Dari Biyar da Tamanin da Takwas (Naira 177,795,588,000).
An ware Naira Biliyan Tamanin da Shida da Miliyan Dari Shida da Hamsin da Uku da Dubu Dari Biyar da Tamanin da Takwas domin aiyukan yau da kullum.
Haka kuma an ware Naira Biliyan Casa’in da Daya da Miliyan Dari da Arba’in da Biyu domin manyan aiyuka.
Cikin kudaden da aka ware domin kasafin shekarar ta 2022 an ware Biliyan 85.88 domin aiyukan cigaban al’umma a bangaren lafiya da ilimi, wannan adadi ya kai kaso 48 cikin 100 na kafatanin kasafin.
An warewa bangaren ilimi Naira Biliyan 57.18 wanda haka ya kai kaso 32 cikin 100 na kasafin, abin da ya haura kaso 26 cikin 100 da Hukumar Majalissar Dinkin Duniya mai Kula da Ilimi da Al’adu ta ce a dinga warewa bangaren ilimi.
Bangaren lafiya kuma an ware masa Naira 28.7 wanda ya haura kaso 16 cikin dari na kafatanin kasafin kudin.