For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Badaru Ya Kaddamar Da Fara Bitar Littafin Koyon Bakin Arabiya Da Hausa

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya kaddamar da fara bitar littafin Koyon Bakin Arabiya da Hausa ga malaman makarantun Islamiyyu na jihar Jigawa.

Badaru wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, Malam Umar Namadi ya baiyana shirin bitar da Kungiyar Malaman Makarantun Islamiyya ta jihar ta shirya a matsayin wani muhimmin mataki na samun cigaba.

Gwamnan ya yi kira ga malaman da su kula sosai wajen bibiyar abubuwan da suke zuwa su zo a makarantun Islamiyyun domin kara inganta tsarin.

Ya kuma tabbatarwa da kungiyar cewa, gwamnatinsa a shirye take wajen cigaba bayar da dukkanin gudunmawar da ta dace wajen cigaban makarantun Islamiyyu a jihar.

A jawabin na Badaru da Umar Namadi ya gabatar, ya ce gwamnatinsu ta gina masallatai na khamsussalawati da na Juma’a sama da guda 900 tare da gina ajuzuwa da makarantun Islamiyyu kusan guda 600.

Tun da farko, a jawabin kungiyar wanda Mataimakin Sakataren Kungiyar, Malam Attahiru Haladu ya gabatar ya baiyana cewa kungiyar tana da manyan bukatu guda biyu, wadanda suka hada da motar zirga-zirgar kungiya da kuma tallafi na musamman ga malaman Islamiyyun.

Babban Malami mai jawabi a taron kaddamarwar, Sheikh Abubakar Gero Arugungun ya yi kira ga malaman Islamiyyun da su yi aikinsu domin neman yardar Allah, inda ya ce, a cikin aikin koyarwar da suke akwai alfarmar duniya da lahira.

Arugungun ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta tallafawa kungiyar da baburan hawa domin samun saukin aikin bibiyar makarantu da kungiyar take yi.

Sauran manyan baki a wajen taron sun hada da kwamishinan ilimi na jihar Jigawa, Dr. Lawan Yunusa Danzomo, Dan Majalissar Tarayya mai wakiltar Birnin Kudu da Buji, Magaji Da’u Aliyu wanda Malam Zubairu Isah ya wakilta, Mai Martaba Sarkin Hadejia wanda Limamin Hadejia, Malam Yusuf Abdurrahman da sauran manyan baki da dama.

Comments
Loading...