For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

BADAƘALAR BILIYOYI: Har Yanzu Abdulaziz Yari Na Hanun EFCC, Yayin Da Aka Saki Ahmed Idris

Dakataccen Babban Akawunta na Ƙasa, Ahmed Idris ya isa wajen iyalinsa bayan Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa da Yiwa Tattalin Arziki Ta’annati, EFCC, ta sake shi.

Ahmed Idris, wanda EFCCn ta kama a ranar 16 ga watan Mayun da ya gabata kan zargin sama da faɗi da kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan 80, an sake shi ne a daren ranar Laraba a matsayin beli.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da bayar da belin ga wakilin DAILY TRUST ta wayar salula a jiya.

“Kawai mun sake shi ne a matsayin beli. Yanzu haka ba ya hannunmu,” in ji Uwujaren a tattaunawarsa da DAILY TRUST.

Ƴan kwanaki kaɗan ne dai bayan kama Ahmed Idris, Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ta sanar da dakatar da shi.

Ministar ta ce, dakatar da shi din ta biyo bayan buƙatar ba shi damar fuskantar abin da ake zarginsa da shi.

A wani ɓangaren kuma, Hukumar EFCCn har yanzu tana riƙe da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda ta kama ranar Lahadin da ta gabata, bisa zarginsa da hannu cikin badaƙalar kuɗaɗen da ake zargin Ahmed Idris da yi.

Wani babban jami’in hukumar ya sanar da wakilin DAILY TRUST cewa, har yanzu Yari ya gaza kammala gabatar da bayanan da ake buƙata kan zarginsa da ake yi ba.

“Zan iya sanar da ku a hukumance cewa, har yanzu Yari yana hannunmu.

“Yana ba mu bayanan da suka dace kan yanda kuɗaɗe sama da naira biliyan 100 suka salwanta daga ofishin dakataccen Babban Akawunta na Ƙasa wanda aka saka ba da jimawa ba,” in ji shi.

Lokacin da aka tunkari mai magana da yawun EFCC kan batun, ya yi alƙawarin yin bayani amma har kawo yanzu bai ce komai ba.

Comments
Loading...