For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Bai Kamata A Ce Kotu Ce Za Ta Bayyana Wanda Ya Ci Zaɓe Ba, Inji Femi Falana

Lauyan Kare Haƙƙin Bil’adama, Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana ya ce, hukuncin Kotun Ƙoli na ranar Alhamis babu abun da yai face kawo ƙarshen duk wata takara, inda ya ce, bai kamata a ce ɓangaren shari’a ne zai bayyana waɗanda suka ci zaɓe ba.

Falana ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a lokacin da ake tattaunawa da shi a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels kan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar Alhamis.

Ya ce, bayyana waɗanda suka ci zaɓe keɓaɓɓen aikin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC ne inda a ce ana yin abubuwa yanda ya kamata a yi su.

Ya ƙara da cewar, babu tantama hukuncin Kotun Ƙoli ya kawo ƙarshen duk wata maganar takara da akai a ɓangaren zaɓen shugaban ƙasa wanda ka yi a watan Fabarairu, to amma wannan hukunci ba yana nufin ɓangaren shari’a ya amince da zaɓen da INEC ta gudanar ba.

Babban Lauyan ya kuma ce, ya kamata Najeriya ta fahimci cewar, idanun baƙaƙen fatar duniya na kanta, saboda haka tana da babban nauyi a kanta wajen gyara kanta domin kar ta kunyatar da baƙaƙen fata a duniya.

Comments
Loading...