For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Bala Umar T.O Zai Kashewa Hadejia Naira Biliyan 2.7 A 2022

Shugaban Karamar Hukumar Hadejia, Abdulkadir Bala Umar T.O, ya ware Naira Biliyan 2 da Miliyan 764 da dubu 853 da Naira 310 a matsayin kasafin kudin Karamar hukumar na shekarar 2022.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin karamar hukumar na shekarar 2022 a ranar Litinin.

A cewarsa, daga cikin kudaden an ware Naira Miliyan 640.4 da domin biyan albashin ma’aikatan karamar hukumar.

Sai kuma Naira Miliyan 800 da dubu 295 da Naira 407 da aka ware domin domin biyan albashin ma’aikatan sashen ilimi na karamar hukumar Hadejia.

Haka kuma, ya ce an ware Naira Miliyan 275 da dubu 330 da Naira 968 domin biyan albashin ma’aikatan sashen lafiya na karamar hukumar.

Bala T.O ya ce an ware Naira Miliyan 510 da dubu 943 da Naira 800 domin gudanar da harkokin yau da kullum a karamar hukumar Hadejia.

Ya kuma ce an ware Naira Miliyan 728 da dubu 851 da Naira 241 a kasafin shekarar 2022 domin gudanar da manyan ayyukan.

Kazalika, ya bukaci mazauna Hadejia, musamman yan kasuwa su rika bawa karamar hukumar hadin kai ta hanyar biyan kudaden haraji.

A Jawabinsa, Shugaban Majalisar Kamsiloli ta karamar hukumar, Isah Abubakar, ya ce majalisar za ta yi abinda ya kamata domin tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin kudin yadda ya kamata.

Comments
Loading...