Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa tsawon shekaru takwas da ya debe yana matsayin gwamnan jihar Kano, bai taba ciyo bashi ba ko na Naira daya.
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan talabishin na ARISE a safiyar Juma’ar nan.
Kwankwaso ya kuma zargi gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da kokari cusa jihar cikin mawuyacin bashi.
Ya ce, yanzu haka ana bin jihar Kano bashin da ya kai Naira Biliyan 187, abun da bayyana a matsayin abun da bai kama a amince da shi ba, domin kuwa mafi yawan aiyukan da ake cewa ana yi a Kano da bashin da ake ciyowa ba aiyuka ne na dole ba.
“A Kwankwasiya, ba mu yarda da ciyo bashi ba har sai ya zamanto babu mafita. Kuma zan fada cewa, lokacin da nake gwamna tsakanin 1999 zuwa 2003 ban ciwo bashin Naira daya daga kowa ba a cikin gida ko kasashen waje.”
“Abin ma da ya faru shine, mun biya duk wata Naira da wadanda na gada suka ciyo a wannan lokacin. Haka kuma lokacin da na kara zama gwamna a 2011, mun sami basussuka wadanda aka ciyo kafin mu dawo, akalla Dala Milyan 200 daga Bankin Duniya a kan abubuwa kamar maleriya, muka cewa Kwamishina ya biya Bankin Duniya da sauran hukumomi, kuma mun biya gaba daya.”