For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Bangaren Malam Aminu Ringim Zai Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli – Danzomo

Jamiyyar PDP reshen jihar Jigawa tsagin Mallam Aminu Ibrahim Ringim za su daukaka kara zuwa Kotun Koli biyo bayan korar kararsu da Kotun Daukaka Kara ta Kano tayi.

Tun asali dai wannan bangare na jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ya shigar da karar uwar jami’yyar PDP ta kasa, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), da kuma jami’an  tsaro bisa zargin su da hada kai da gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar PDP na  kananun hukumomi da kuma na jihar Jigawa ba tare da an gudanar da zabukan shugabannin mazabu ba a cewarsu.

Haruna Shu’aibu Danzomo, mai magana da yawun bangaren Malam Aminu Ringim ya bayyanawa Taskar Yanci cewa, abun da suke zargin “ya sabawa Kundin Tsarin Mulki na Jamiyyar PDP ta Kasa dama Kundin Tsarin Dokoki na Zabukan Shuwagabannin jamiyyar na shekarar 2020 da aka sabunta.”

KU KARANTA: Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Uwar Jam’iyyar PDP Ta Kasa

Tun asali dai wata karamar kotu a jihar Jigawa ta dakatar da zabukan kafin daga bisani ta ce ba ta da hurumin sauraren wannan kara saboda rikici ne da ya shafi cikin gida a jam’iyyar.

Sai dai bangaren Mallam Aminu Ibrahim Ringim ya daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara da ke Kano wadda a yau tayi hukuncin cewa, ta goyi bayan hukuncin kotun baya, yayinda tai watsi da karar.

Haruna Shu’aibu Danzomo ya bayyanawa Taskar Yanci cewa, “bangarenmu na Siyasa da Kulawa mun kara hada takardunmu domin zuwa Kotun Koli ta (Supreme Court) domin samun hukunci na karshe.

Comments
Loading...