Daga: Muhd Yobe
A cigaba da buga gasar matar shugaban kasa Muhamamad Buhari, Aisha Buhari da ake fafatawa, a yau an gwabza a wasan karshe tsakani kungiyar kwallon kafar matan Nigeria Super Falcons da Banyana Banyana ta Afrika ta kudu, wasa ne da aka fafata a filin wasa na Mobolaji Johnson dake Birnin Legas.
Tunda farko Super Falcons ce ta fara cin gidanta ta hannun ‘yar wasan bayan kungiyyar ta gefen dama Olozie Michele a minti 5 da fafatawar, sai Motheo Linda ta kara kwallo ta 2 a cikin minti na 18, Salgado Gabriella 43, Haka dai akaje hutun rabin lokaci Afrika ta kudu na da ci 3 Nigeria na nema.
Bayan andawo daga hutun rabin lokaci Nigeria ta warware Kwallaye 2, dukkanin su ta hannun Cigaba Ikechukwu a mintina na 47 da 53 daga karshe, Banyana Banyana ta zura kwallo ta 4 ta hannun Magaoa Hilda a mintina na 86.
Da wannan nasarar yanzu ta tabbata cewa South Africa ta lashe wannan Gasar.