For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Bauchi Ta Shigar Da Dogara Da Wasu Mutane 28 Kara Kan Rikicin Tafawa Balewa

Gwamnatin jihar Bauchi ta dau matakin shari’a a Babbar Kotun Jihar Bauchi tana zargin Yakubu Dogara da wasu mutane 28 kan kisan kai da barnata dukiyoyi bayan taron tunawa da Baba Peter Gonto karo na 21 a kananan hukumominTafawa Balewa da Bogoro na jihar Bauchi.

A baya dai, jaridar Vanguard ta rawaito cewa, tsohon Kakakin Majalissar Wakilai, Yakubu Dogara ya rubuta takarda zuwa Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, da kuma Babban Sufeton ‘Yansanda inda ya gargade su kan barazanar tsaro idan har aka bari taron tunawa da Baba Gonto ya gudana.

Cikin korafe-korafe shadayan da jaridar Vanguard ta leko, an zargi Dogara da sauran mutane 28 laifin yin shiri domin cutar da mutane a yankin domin kawo cikas ga bikin tunawa da Baba Gonto.

KU KARANTA: Helkwatar Tsaro Ta Ce An Kashe ‘Yan Ta’adda 950 Da ‘Yan Bindiga 537 Cikin Watanni Bakwai

Zarge-zarge shadayan an rubuta su kamar haka: “La’akari da Sashi 98 (1) da (2), 100 (b) da 103 (b) na Dokar Manyan Laifuka ta Jihar Bauchi ta shekarar 2018. Laifi na daya: Kai Yakubu Dogara, namiji dan Maitama a Abuja Babban Birnin Tarayya, Air Commodore Ishaku Komo Mai Ritaya, namiji dan Titin Kaduna zuwa Abuja a Jihar Kaduna, Rabaran Markus Musa, namiji dan Garin Tafawa Balewa, Peter Emmanuel, namiji dan Garin Tafawa Balewa, Ga’Allah Daniel, namiji dan Garin Tafawa Balewa, Iliya Emmanuel, namiji dan Garin Tafawa Balewa . . . .

“A ranar ko tsakanin ranakun 29, 30 da/ko 31 ga watan Disamba na shekarar 2021 kun amince ku aikata ko ku jawo a aikata mummunan aiki: ko hada kai tsakaninku da wasu kari ku zuga Matasan Garuruwan Tafawa Balewa da Bogoro su hana zaman lafiya ta hanyar kona gidajen mutane, toshe hanyoyi, kai hari kan wadanda aka gaiyata da sauran mahalarta bikin tunawa da Marigayi Baba Peter Gonto da kuma kaddamar da littafi a garin Bogoro inda aka kona duk kayayyakin da aka tanada domin bikin, hakan ya sanya aikata laifi da ya saba da Sashi na 96 wanda hukuncinsa ke Sashi na 97 Kundin Dokar Manyan Laifuffuka na jihar Bauchi.

Comments
Loading...