For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Bayan Shekaru 40, Huzaifi Ya Ajjiye Aikin Jan Sallar Tarawihi A Masallacin Annabi

Sheikh Aliy Ibn Abdurrahman Al-Huzaifi ba zai ci gaba da jan sallar Tarawihi ba a Masallaci Mai Alfarma na Annabi da ke Madina.

Wannan na nuni da cewa Shehin ba zai ja sallar Tarawihi ta azumin bana (1443) ba wanda ake sa ran farawa ƴan kwanaki masu zuwa.

A wani rubutu na shafin Haramain Sharifain an baiyana cewa, “Bayan shekaru da dama, . . . Sheikh Ali Al Hudaify ba zai ja sallar Tarawihi ko Tahajjudi a Masallacin Annabi bana ba.”

Binciken da NIGERIAN TRACKER ta yi ya nuna cewa, sanannen malamin ya fara jan sallar Tarawihi ne a shekarar 1981 a Masallacin Annabi (S.A.W).

Dattijon Limamin mai shekaru 75 a duniya, yana karanta Al-Qur’ani da murya mai dadi wadda take ɗaukar hankalin masu sauraronsa, haka kuma miliyoyin Musulmai ne ke sauraronsa a duk fadin duniya.

Shafin Haramain Sharifain bai baiyana dalilin janye Al-Huzaifi daga jan sallar Tarawihin ba, sai da ta iya yiwuwa hakan na da alaƙa da tsufa.

A wajejen shekarar 2016 ne Masarautar Saudiyya ta janye Babban Malami mai Fatawa, Abdul Aziz Abdullahi Ali Sheikh daga jagorantar huɗubar Arfa a lokacin Hajji saboda tsufa, bayan ya ɗebe shekaru 35 yana kan wannan aikin.

(NIGERIAN TRACKER)

Comments
Loading...