Bayan kwashe shekaru sama da bakwai a karagar mulki, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ministocinsa aikin samar da “Cikakken Tsarin Aiwatarwa Domin Kare Matsalar Ambaliyar Ruwa a Najeriya.”
Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya umarci Ministan Albarkatun Ruwa da Ministocin Muhalli da na Sufuri da kuma gwamnatocin jihohi da su samar da tsarin.
Jihohin Najeriya da dama na fama da matsalolin ambaliyar a lokacin damuna, abun da ya fi kamari a bana tun bayan shekarar 2012.
Ambaliyar ruwan ta kuma jawo asarar rayuka sama 600 da kuma rasa muhalli ga iyalai sama da miliyan guda.
Ambaliyar ruwan dai na faruwa ne bisa matsalolin sauyin yanayi da kuma gurbatattun aiyukan kula da muhalli a bangaren al’umma, da kuma yin kunnen kashi ga bayanan gargadin da hukumomi ke bayarwa akan matsalar.
Garba Shehu ya ce, umarnin shugaban kasar an mika shi ne ga ministan a takardar da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari ya sanyawa hannu.
Shugaban Kasar ya kuma bayar da umarnin cewa a gabatar masa da rahoton yanda za a yi cikin kwanaki 90 masu zuwa, abun da zai ba shi damar aiwatarwa cikin kasa da watanni biyar da zasu rage masa a lokacin, kafin barinsa ofis a watan Mayu na 2023.