Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, ya kare matakin da gwamnati ta dauka na kin bayyana sunayen masu temakawa ta’addanci a halin yanzu. Ya ce hakan ya zama tilas domin kada a kawo cikas ga bincike.
Babban Lauyan ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin New York, a cewar wata sanarwa da kakakinsa, Umar Gwandu, ya fitar a ranar Laraba.
Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, a baya, ya ce gwamnati ba ta da sha’awar bayyana sunayen mutanen da ake zargi sai dai za ta gurfanar da su a gaban kotu.
Gwamnatin Tarayyar ta sha suka a kwanakin nan saboda ta ki bayyana sunayen masu temakawa ta’addancin duk da taimakon bayanan da Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashe suka ba wa kasar.
Da yake mayar da martani kan takaddamar da ke ci gaba da ta’azzara, Malami ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi aiki tukuru don ganin babu abin da ya rage da ake bukata don gurfanar da masu hannu a Boko Haram da kuma kawo cikas a yaki da ta’addancin da ake a kasar.
Ya ce, “Lokaci bai yi ba na tonon asirin, domin gudun kar a kawo matsalawa binciken da ake yi.
“Muhimmin abin har yanzu shine, samuwar zaman lafiya da cikakken tsaro na kasarmu.
“Dangane da batun daukar nauyin ta’addanci, mun yi nasarar gano wadanda ake zargi da alhakin samar da kudi ga ‘yan ta’addar, kuma muna toshe hanyoyin da ke da alaka da hakan yayin da muke gudanar da bincike mai tsanani wanda hakika yana tasiri sosai dangane da yaki da ta’addancin.
“Gaskiyar magana ita ce ana bincike kuma ana samun ci gaba. Don kare manufar binciken, ba zan so in zama mai yin abin da zai haifar da matsala ga nasarorin da muke samu ba.”
Malami ya ce duk abin da gwamnati ke yi dangane da tsarewa da kuma kame masu laifi, ana yin su ne bisa tsarin shari’a.
Ya kara da cewa cutar COVID-19 da yajin aikin watanni biyu da Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya ta yi a farkon shekarar nan ya shafi batun gurfanar da masu daukar nauyin Boko Haram.
Malami ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin masu gabatar da kara na tarayya a ofishin Babban Lauyan Najeriyar, ta sake duba fayilolin kararrakin da suka shafi Boko Haram har sama da 1,000 wadanda daga ciki aka gurfanar da 285 a gaban Babbar Kotun Tarayya bisa zargin ta’addanci.