Daga: Baba Alhaji Ashbab
Menene Rai Dore/Majanfari?
Rai dore wata karamar ciyawa ce koriya, tana da tsayin da ya kai na mita daya da digo takwas (1.8m). Ganyen rai dore na da launin kore mai haske (light green) a sanda take girma, a yayinda ta kosa kuwa, ganyen kan canza launi ya koma dark brown.
Ciyawar takan fito ta girma a wasu daidaikun wurare masu danshin sanyi kamar a lambuna, bakin gulbi ko a cikin daji a lokutan damina. Tana fitowa sau uku a cikin shekara.
Da Turanci ana kiranta da coffee sena. A kasar Jamus ana kiranta da suna kaffee kassie. A kasar India tana da suna kasounda. A China suna kiranta da wang-jiang nan. A harshen faransanci ana kiranta da suna bentamar. A yayinda a harshen Hausa ake kiranta da suna ‘rai dore’ ko ‘majanfari’ a Hausar wasu jahohi, kamar a Sokoto suna kiranta da suna ‘sanga-sanga’.
Sananniyar ciyawace da aka dauki dimbin shekaru ana amfani da ita a kasashe da dama a fadin duniya kama daga kasar India, Kudancin Amurka, Brazil, China, Germany, France, Jamaica, da kuma kasashen nahiyar Africa.
A kasar Hausa an fi amfani da ganyen wannan ciyarwa don maganin zazzabin Typhoid wato typhoid fever a turance da kuma masu ciwon shawara. sai dai amfanin wannan ciyawar ya fi gaban haka.
A kimiyance tana daukeda sinadaran dake maganin wasu kwayoyin cuta wato chemical properties kamar su: funiculosin, kaempferol, lignoceric acid, linoleic acid, oleic acid, xanthorin, quercetin, physcon, obtusin, tannic acid, emodin, cassiollin, a phytosphanol, physcion, occidentol I.

Maganin Da Ake Yi Da Ganyen Rai Dore
Saiwar ciyarwa tana maganin zafin dafi na cizon kunama da maciji da sauran kwari.
Saiwar rai dore na maganin toxins da poison. Idan an sha kananzir ko wani sinadari mai illatar da jiki.
A kasar Brazil, suna amfani da rai dore dan maganin rashin lafiya kamar na zazzabi, tarin tibi, matsalolin hanta. suna kuma ciza ganyenta su tauna su shafa akan wani rauni ko kurji.
Rai dore na maganin gani garara-garara, kaikayin fatar jiki, bayan gida mai tauri, kumburin hanji (intestinal inflammation) sannan yana maganin cutukan fata (skin diseases).
Yana maganin tarin Asthma, da sanyin kirji (chest cold), yana maganin basir mai tsiro, yana maganin tsutsotsin ciki (anti helminthic) ana dafa ganyen ko a shanya ganyensa idan ya bushe sai a gauraya da ganyen lalle a kwaba a yi amfani dasu dan kara armashin fata.
Illolin Amfani Da Rai Dore/Majanfari
Ba a bukatar Masu juna biyu ko masu shayarwa su sha rai dore amma zasu iya amfani da shi suyi suraci/salace domin magance ciwon jiki, ko malaria. Amma kada su sha domin yana motsa mahaifa, sannan idan mai shayarwa ta sha to shima yaron zai sha ta hanyar shan mama wanda wannan akwai illa a gareshi sosai dan zai iya janyo masa wani abu na daban.
Haka kuma kada a maida rai dore tamkar abinci ta yanda duk inda aka motsa sha ake yi, ba abinci bane, maganine da ake amfani da shi kawai a lokacin da ake da bukata.
Ina karo janyo hankalinmu da mu kula ba komai kake jin labari ko kake gani a kasuwa ko a bakin tituna na yawo ka siya ka je kana sha ba. A san abinda ake sha, akwai bukatar asan ciwo a kuma san inda za a nemi maganinsa.
Baba Alhaji Ashbab
Ya Rubuto Daga Hadejia, Jigawa