Shiga cikin yanayin damuwa, na iya kara hatsarin kamuwa da ciwon suga kala na biyu (type 2 diabetes) ko da kuwa mutum yana yin rayuwa cikin kulawa da lafiyarsa.
Binciken da aka gudanar a kan ‘yan Birtaniya mutum 300,000, ya gano cewa, wadanda suke cikin farinciki a lokuta mafi yawa, suna mataki na uku wajen nuna shiga matsanancin hatsari.
Haka kuma, irin wadannan mutane suna mataki na biyar wajen samun bugun zuciyar da ya saba ka’ida wanda ka iya kai wa ga bugawar zuciyar.
Hatsarin da yake tattare da wadannan mutane bai karu ba ko da an yi la’akari da sauran dalilai kamar abinci, nauyi, shan taba da kuma zubin kwayoyin halitta.
Masu binciken sun ce, bincikensu ya nuna cewa, matsalar da ake bincike a kai (damuwa) na bayar da gagarumar gudunmawa wajen samun matsalolin da suka danganci zuciya da sauran matsalolin da suka shafi lafiya.
Lokacin da wani ya tsinci kansa a damuwa, bacin rai, ko takura, bugun zuciyarsa na karuwa da kuma gudun jinin jikinsa, hakan na sa jikinsa ya haifar da karuwar sinadarin cortisol, kwayar halittar damuwa, kuma hakan na karuwa zai haifar matsalolin zuciya.
Masu bincike a Babban Asibitin Massachusetts, Makarantar Nazarin Harkokin Lafiya ta Harvard da kuma Jami’ar Yale duk na kasar Amurka, sun duba bayanan mutane 328,152 wadanda ke tsakanin shekarun 40 zuwa 69 a matattarar bayanai ta UK Biobank.
Sama da kaso 3 cikin 4 na mutanen, wato kaso 77.7% sun baiyana cewa ba su tsinci kansu a cikin damuwa ba, yayin da kaso 18.3% suna tsintar kansu cikin damuwa wasu lokutan.
Kusan kaso 4% sun baiyana cewa suna yawan shiga damuwa.
Ta hanyar amfani da wadannan bayanai, sun kirkiri wata na’ura ta musamman da za a na amfani da ita wajen kare hatsarin kamuwa da cutar zuciya.
Masu binciken sun gano cewa, karancin samun kai a damuwa na da alaka da karancin hatsarin kamuwa da da cutukan da suka shafi jijiya, ciwon suga kala ta biyu, da kuma bugun zuciyar da ya saba ka’ida da kaso 34%, 33% da kuma 20%.
Masu binciken sun ce, sakamakon binciken bai shafi hatsarin da kwayoyin halittar mutum kan iya haifar masa ba wajen kamuwa da cuta.
An wallafa wannan binciken ne a mujallar ilimi ta Nature Cardiovascular Research.
Masu binciken sun ce, bayanan yanda damuwa kan haifar da cututtukan da suka shafi zuciya har yanzu ‘ba a gama gane shi ba”.
Sun baiyana cewa, sakamakon bincikensu ya gano cewa, magance shiga damuwa zai iya rage hatsarin kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya.
Haka kuma, sun baiyana cewa, ana bukatar karin bayanai domin gane cewa ko magance shiga damuwa na iya rage hatsarin kamuwa da cutar zuciya, suga da bugun zuciyar da ya haura ka’ida.
A wani binciken da aka wallafa tare da wannan bincike, masanan matsalolin zuciya a Jami’ar Cambridge, Dr Scott Ritchie da Dr Michael Inouye sun ce, sakamakon binciken ya nuna “shaidar farko ne” cewar damuwa da danginta na kara hatsarin kamuwa da cutar zuciya da kuma ciwon suga kala ta biyu sama da tsarin gudanar da rayuwa da kuma gadon kwayoyin halitta.
Binciken ya kuma bayar da shawarar sabbin hanyoyin magance matsalar kamar bincikar damuwar mutane da hanyar bukatar amsa tambayoyin da ba sai an kashe kudi da yawa ba domin kara ganowa da kuma kulawa da matsalolin da suka shafi cutttukan zuciya.
(Mail Online)