For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Birtaniya Ta Cire Najeriya Daga Jerin Kasashen Da Ba Za Su Shigeta Ba

Gwamnatin Kasar Birtaniya a ranar Talatar nan ta ce dukkanin kasashe 11 ciki har da Najeriya za su fita daga jerin kasashen daga aka harmtawa shiga kasar daga karfe 4 na safiyar Laraba.

Kasashen Angola, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Namibia, Najeriya, South Africa, Zambia da Zimbabwe na cikin jerin kasashen.

Birtaniya ta dawo da shigar da kasashe cikin jerin kasashe masu hatsari ne a karshen watan Nuwamba saboda bullar samfurin Omicron na Korona.

Sai dai kuma BBC ta rawaito cewa, Sakataren Lafiya, Sajid Javid ya ce samfurin ya yadu da yawa ta yanda dokar hana shiga kasar ba ta da wani tasiri.

Sajid ya sanar da majalissar wakilai ta Birtaniya cewa, “yanzu haka akwai yaduwar Omicron a tsakanin al’ummar Birtaniya, sannan kuma Omicron ta yadu da yawa a duniya, hana shiga kasar yanzu bai da tasiri wajen hana shigar cutar kasar daga kasashen waje.”

“Yayin da za mu cigaba da daukar matakan kariya kan masu shigowa daga kasashen waje, za mu tsame kasashe 11 daga cikin wadanda muka aiyana a matsayin masu hatsari wadanda ba za su shigo ba daga karfe 4 na safiyar gobe.”

Comments
Loading...