For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Birtaniya Ta Saki Sunayen Marigaya ‘Yan Najeriyar Da Suke Da Dukiya A Kasar

Gwamnatin Birtaniya ta wallafa a kalla sunyen mutanen da suka mutu 56, ‘yan asalin Najeriya, wadanda ke da dukiyoyin da magada ba su nema ba a kasar.

BUSINESS DAY ta bayyana cewa, wannan ya bayyana ne a shafin yanar gizo na Lauya Mai Kula da Dukiyoyin da Aka Mutu Aka Bari a Birtaniya, Susanna McGibbon.

Rahoton ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda suka dade da mutuwa shine Mark N’wogo, dan Najeriya wanda aka haifa a Sapele na Jihar Delta, kuma ya rasu ne tun ranar 9 ga watan Disamba na shekarar 1992, a garin Surrey da Birtaniya.

To amma, har yanzu kusan shekaru 30 da mutuwarsa, babu wanda ya bukaci tarin dukiyar da ya mutu ya bari, dukiyar da a watan Disamba zata zama mallakar kasar Birntaniya.

Jerin sunayen gidaje da sauran gine-ginen da ba a samu masu nema ba wadanda ofishin mai kula da dukiyar da aka mutu aka bari ya sabunta a ranar 8 ga watan Satumba, 2022, ya bayyana N’wogo a cikin sauran ‘yan Najeriya 56 da suka mutu ba tare da an nemi dukiyoyinsu ba.

A cikin sunayen akwai wani mai suna, Victor Adedapo Olufemi Fani-Kayode, wanda aka ce ya mutu a ranar 15 ga watan Agusta, 2001 a Birmingham.

Akwai kuma Arbel Aai’Lotta ‘Oua Abouarh wanda ya mutu a ranar 5 ga Fabarairu, 1998 a Chiswick, London.

Bayanai a kansa sun nuna cewa, ya yi aure a watan Disamba, 1959 a gurin da ba a sani ba, sannan yana da yara hudu da ba a gano su ba.

Bayanan sun kara nuna cewa, an haifeshi a Arewacin Najeriya a wajejen 3 ga watan Maris, 1930, kuma iyayensa sune Alfred Hallim Abouarh da Addanue Abouarh Nee Onwudachi.

Akwai kuma Paul (Akinola) Bernard wanda aka haifa a Lagos ya mutu a London a ranar 12 ga Oktoba, 2008, wanda kuma bayanai suka nuna ya auri mata ta biyu mai suna, Marie Vidarte de Castro a shekarar 1970, amma ita ma ta mutu a Agusta, 2008, sannan kuma yana ‘ya da matarsa ta fari wadda suka rabu tun shekarar 1970.

Sai John Olaolu Bankole, wanda aka haifa a Ibadan a ranar 2 ga Agusta, 1958, ya rasu a London a ranar 27 ga Afrilu, 2010, bayanan da suka shafe shi sun nuna cewa a kashe aurensa a ranar 11 ga Nuwamba, 2002, yayin da takardar shedar aurensa ta nuna cewa, sunan babansa Oladipupo Bankole.

Shi kuma Enwukwe Graham Kwedi Edde, wanda ya mutu a ranar 6 ga Janairu, 2011 a London, abun da aka sani game da shi shine an haife shi a Diobu ta Jihar Rivers; Sai Charles Ayodele Aliu wanda ya mutu a ranar 31 ga Maris, 2011 a Solihull, West Midlands, an ce yana da ‘yan uwa a Najeriya.

Akwai kuma Sunny Eyo Edem, wanda ya mutu a ranar 16 ga Satumba, 2011 a Fulham, an ce akwai yiwuwar yana da da namiji da kuma ‘yan uwa a Calabar ta Najeriya.

Sai William Kadry, wanda ya mutu a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2011 a Fulham, an ce an haife shi a Iponri, Jihar Lagos, sannan babansa Akanni Kadiri ya mutu a 1941, yayin da mahaifiyarsa Muniratu Kadiri ta mutu a 1958.

Wadanda suka mutu ba jimawa sun hada da Solomon Adekanmibi, wanda ya mutu a ranar 31 ga Janairu, 2021 a Colchester, Essex; Sai Eugene Bucknor, wanda ya mutu a ranar 2 ga Maris, 2021 a Brockley, London; sai Jeff Adhekeh, wanda ya mutu a ranar 12 ga Maris, 2021 a South Kensington, London; da kuma Louisa Holmes, wanda ya mutu a ranar 24 ga watan Mayu, 2021 a Cheam Sutton.

Comments
Loading...