For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Boko Haram Ta Kashe Masunta 35 A Borno

Akalla masunta 35 ne wadanda suka fita kamun kifi, ‘yan Kungiyar Boko Haram suka kashe a Karamar Hukumar Ngala da ke Jihar Borno.

Mazauna garin da dangin wadanda aka kashe sun ce, sun matukar kaduwa da harin, yayin da sukai kira da a samar da karin tsaro a yankin domin kare su daga ‘yan ta’addar.

Gwamnatin Jihar Borno da Masarautar Dikwa sun tabbatar da kisan da akai wa masunta tare da mika ta’aziyyarsu ga ga iyalan marigaya da kuma yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Majiyoyi da dama sun sanar da DAILY TRUST cewa, mayakan Boko Haram din sun sha yi wa masuntan gargadi kan cewa su dena shiga yankin mayakan don kar su jawo kansu matsala, amma saboda neman abin da zasu kula da kansu da shi, masunta ba su da zabi sai sun fita kamun kifin.

A ranar Laraba, mayakan na Boko Haram sun bude wuta a kan masuntan a kusa da gabar kogi, inda suka kashe akalla masunta 35 tare da ji wa da dama raunuka, wasu kuma da yawa sun bata.

Comments
Loading...