For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamna Badaru Abubakar Kan Yadda Darajar Ilimi Take Narkewa A Jigawa

Daga: Ahmed Ilallah

Maigirma Gwamna, bayan gaisuwa marar adadi, ina tayaka murnar kaddamar da ginin sabuwar makarantar UBEC Smart School wanda kayi a garin Hadejia. Sai dai kamar yadda aka sani ana cikin wannan biki amma, wasu ‘yayanka na kuka saboda basa zuwa makaranta.

Yara yan makarantar da suka kamala karatun su na Primary da yaran da suka kammala karatun su na karamar Secondary har yanzu suna zaune a gida ba tare da sannin makomar su ba. Kafin su rubuta jarrabawar kammala makarantun su sai da suka kai bayan shekarar gamawar su.

Maigirma Gwamna, kamar yadda ya ke a jadawalin lokutan kararatu a Jigawa, a yanzu dai dalibai na zango (term) na biyu ne, wanda kusan saura wasu satuka shima zangon ya kawo karshe, wanda duk tsawon wannan lokacin an gaza fiddo da sakamakon jarrabwar da yaranan suka yi a zangon da ya gabata, wannan ba karamin hatsari bane a rayuwar wadan nan yaran dam cigaban harkar ilimi a Jigawa.

Maigirama Gwamna, ba karamin hatsari bane a bar yara a wannna matakin shekaru suna garagamba a gari ba tare da zuwa makaranta ba, kuma zai yi wuyar gaske a samu ‘yayan masu fada a ji ace suma yaran su basa zuwa makaranta saboda wannan dalilin.

Maigirma Gwamna, a tarihin Jigawa, wannan ne mummunan lokacin da yara dalibai, masu gama primary da karamar Sakandaare suka sami kansu a wannan yanayi, wannan ya kasance tarihi mafi muni da ba mu so mu ji shi ba.

Maigirma Gwamna, a tsawon shekaru, tun kafin zuwan gwamnatin ka, jahar Jigawa na fama da matsalolin na rashin ingancin koyar wa da ma rashin ingancin wasu malaman makarantar, sai ga a wannan shekarun kuma makarantun Jigawa na fama da rashin isassum malaman makaranta, wannan matsala kuma ta shafi kusan duk nau’in makarantun dake Jigawa, kama da primary zuwa makarantun gaba da sakandare. Wannan matsala ba karamin tasgaro ta kawo ba a cigaban ilimi a wannan jahar.

Maigirma Gwamna, tabbas wannan gwamnatin tayi kokari, musamman na samar da makarantu kananan Sakandare sama da dari da kuma manyan makarantun Sakandare sama da arbain (40) a fadi Jahar Jigawa, wannan ba karamin kokari aka yi ba.

Amma yana da kyau mu tuna cewa gina makaranta kadai ba zai sanya kowa ce jaha cimma burinta akan ilimi ba, tabbas wannan makarantu suna bukatar sauran kayan aiki da ya kamata don inganta harkar koyo da koyar wa, musamman malaman da za su koyar. Mafi akasirin wadannan makarantu basu da laboratory do koyon ilimin kimiya, wanda wannan shima ba karamin nakasu zai kawo ba a harkar ilimi a wannan jahar.

Maigirma Gwamna har yanzu akwai gazawar fahimtar al’umma a kan tsari da manufar ilimin jahar Jigawa ta yadda zai kawo cigaban al’ummar ta da kuma jahar a matsakaici da dogo zango.

Dukka jahar da take so ta kawo karshem matsalolin al’umar ta daga rashin tsaro, talauchi, rashin aikin yi da ma sauran matsalolin rayuwar al’umma ta yau da gobe dole sai ta bunkasa harkar ilimin al’ummatta, tun daga primary zuwa manyan makarantu.

Ilimi bazai inganta ba, har sai gwamnati ta bashi muhimmanci, wajen sauke nauyin da ke kanta na samar da abubuwan da suka zama dole don koyo da koyarwa. Ya kamata a duba yanayin da yaran nan suke ciki.

Maigirama Gwamna, wadannan suna daga cikin matsalolin da suke narkar da darajar ilimi a sannu a wannan jaha tamu.

Allah ya kyauta.

alhajilallah@gmail.com

Comments
Loading...