Zuwa ga jaridar TASKAR YANCI. Ku temaka ku wallafamin wannan wasika tawa, ta yanda za ta isa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
Shimfida
Mai Girma Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, Gwamnan Jihar Jigawa, barka da aiki, ina rokon Allah Ya cigaba da yi maka jagoranci a al’amuranka.
Mai Girma Gwamna, na rubuta maka wannan wasika ne domin na wakilci dalibai, malamai, iyaye, ‘yan’uwa, da dinbin masu kaunar karatun Al-Kur’ani na jihar Jigawa, Najeriya da ma duniya baki daya kan kan kiraye-kiraye guda biyu.
Tuna Baya
Kafin na bayyana kiraye-kirayen, Mai Girma Gwamna, ni daya ne daga cikin dinbin ‘ya’yan talakawan da suka wakilci jihar Jigawa a gasar karatun Al-Kur’ani ta kasa, kuma na yi wakilcin jihar har sau hudu, a shekarar 2004, 2005, 2006 da kuma 2013.
Shekaru ukun farko da nai wakilci, sun kasance zamanin tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Ibrahim Saminu Turaki. Kuma ina iya tuna cewa, a wadannan shekaru, ‘yan takarar jihar Jigawa ba komai ba ne a gasar ta kasa, har ma da zarar an kira dan jiharmu don ya yi karatu, sai ka ga ‘yan kallo suna ficewa domin su sami hutu kafin a kira ‘yan takarar da aka san za su tabuka abin kirki.
Mun Sha Wuya
Kimarmu a matsayin ‘yan jihar Jigawa kadan ce, saboda rashin wadatar gatan da muke samu daga jiharmu. Ina iya tunawa, a shekarar 2004, mun je jihar Kebbi ne gasar ta kasa, kuma an kai mu a wata tsohuwar mota J5 ta makarantar Kwalejin Koyon Kasuwanci da Mulki ta Hussaini Adamu, wadda a yanzu ta koma Jigawa State Polytechnic, Dutse.
Sau uku tayar motar tana fashewa a hanya, saboda tsufan motar da kuma rashin kyawun hanya, har ma a hanyarmu ta dawowa Jigawa, dare yai mana a hanya bayan barinmu Sokoto kadan. Aka fara tunanin ko za mu tsaya mu kwana a Gusau zuwa safiya mu dora, amma rashin kudin wajen da za a kama mana ya sa muka wuce, ba mu zo Kano ba sai lokacin sallar Asuba.
Tafiya ce mai nisa da wahala saboda karancin tanadi, sannan kuma tafiya ce mai karancin nasara, saboda ‘yan Jigawa mu goma da mukai wakilci, babu ko daya da ya zo ko na biyar ne a wannan gasa.
Shekaru biyun da suka biyo baya ma haka abun ya kasance, duk da zan iya cewa an samu sauki, kasancewar a jihohi makwabta a kai, wato Kano da Bauchi, haka kuma a Kano mun samu na biyu shi kadai, a Bauchi kuma ni kadai na yi na hudu.
Babu Mashawarta Ga Gwamnati
Mai Girma Gwamna zan iya alakanta abun da ya faru a wadancan shekaru da karancin masu baiwa gwamnati ingantacciyar shawara kan samar da cigaba mai ma’ana.
Muna godewa Allah kan cewa yanzu akwai masu kishi da jajircewa a harkar tun daga kan Kwamishina, Dr. Lawan Yunusa Danzomo, Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu, S.A Sabo Muhd Yankoli, S.A Ibrahim Garba Babalolo da sauransu duk abokan shawararka ne, kuma suna da inganci.
Mafi Yawanmu ‘Ya’yan Talakawa Ne
Mai Girma Gwamna, bari na yi anfani da wannan dama, na sanar da kai cewa, mafi yawanmu masu shiga gasar karatun Al-Kur’ani ‘ya’yan talakawa ne, wadanda iyayensu ba su da karfin iya yi musu gata kamar yanda masu hannu da shuni suke yiwa ‘ya’yansu. Ilimin zamanin ma muna samu ne gwargwadon karfin guiwa da juriya da kuma hangen muhimmanci, ba wai don hanyar samun tana da sauki a garemu ba.
Tsarin Gwamnatin Sule Lamido
Mai Girma Gwamna, na san ka gaji wani tsari da gwamnatin Alhaji Sule Lamido ta zo da shi na tura duk wanda ya zo na daya a gasar karatun Al-Kur’ani matakin jiha, karo karatu a kasashen waje.
Wannan tsari, Mai Girma Gwamna, ya kawo gagarumin cigaba a harkar gasar karatun Al-Kur’ani a Jigawa, domin ya samar da masu zurfin ilimi da dama har a matakin PhD. wadanda suke bayar da gudunmawa wajen cigaban jihar Jigawa, musamman a fannin ilimi, tarbiya da kuma zaman lafiya.
A wancan tsari na gwamnatin Sule Lamido, ana tura mutane goma ne duk shekara domin su karo ilimi a fannoni da dama na rayuwa da suka hada da Ilimin Addinin Musulunci, Larabci, Kimiyya, Yada Labarai, Likitanci, Fasahar Zamani da sauransu.
Wannan tsarin ya kawo cigaba matuka a fannin samun nasara a gasar kasa, ina iya tunawa a shekarar 2013 jihar Jigawa ta ciyo motoci biyar, kujerun aikin hajji biyar sannan kuma ta kara wakiltar Najeriya a gasar karatun Al-Kur’ani ta duniya.
A wannan lokaci an kai mu a doguwar lafiyayyiyar mota ta alfarma irin wadda ‘yan majalissu suke hawa, an kamawa malamanmu hotel na alfarma an kuma ba mu alawuns mai kyau.
A wannan lokacin ko’ina aka ganmu sha’awarmu ake yi, ana son a yi abota da mu, ana karramamu, ana ganin kwarjininmu, uwa uba dakin karatun gasar kasa cika yake makil idan an kira dan jihar Jigawa zai yi karatu, saboda an san mun zama gwanaye.
Matsin Tattalin Arziki Ya Kawo Matsala
Mai Girma Gwamna, na sani cewa, zuwan gwamnatinka, saboda kalubale na matsin tattalin arziki, an dakatar da wannan tsari, amma duk da haka an cigaba da kulawa da wadanda suka sami fitar kafin dakatarwar, muna godiya da hakan sosai.
Kowa ya fahimci matsalar, ganin yanda farashin mai ya sakko kasa sosai a wancan lokacin, haka kuma darajar naira ta kara faduwa.
Muna godewa Allah bisa samun sauki a yanzu, musamman saboda jajircewarka wajen farfado da tattalin arzikin Jigawa.
Akwai Wata Matsalar
Mai Girma Gwamna, tabbas akwai matsala kuma jihar Jigawa tana yin asarar kwararru kuma masu kishi da son saka alkhairin da akai musu. Na fadi hakanne saboda tuno cewa, da yawa daga cikin wadanda suka ci moriyar wancan tsari, suna zaune a gida ba sa aiki, ko kuma sunayin wanda gudunmawar da suke bayarwa ba ta kai wadda ya kamata su bayar ba. Wadansunmu suna koyarwa a Islamiyyu ne inda suke dogaro da kudin wata domin cin abinci.
Mai Girma Gwamna, mun samu fita kasashen waje, kuma mun kallo cigaba da yawa da duniya ta samu, mun kuma kallo abubuwa da zukatanmu ba iya idanuwanmu ba, sannan mun dawo da burin tayaku ciyar da jiharmu gaba, amma da yawanmu, mun rasa damar hakan.
Kirana
Kirana kuma kiran duk masu ruwa da tsaki da Al-Kur’ani a Jigawa, Najeriya da ma duniya shine, Mai Girma Gwamna ka dawo da tsarin nan na tura ‘yan musabaka karo karatu waje, musamman saboda ganin cewa bisa kokarinka, tattalin arzikin Jigawan ya daidaita – dadin dadawa kuma gwamnatinka ta fifita cigaban ilimi kan komai a kasafin kudin bana, tabbas wannan abin yabawa ne.
Haka kuma, Mai Girma Gwamna, ka temaka ka baiwa wadanda suka kammala karatunsu suka dawo damar temakawa wajen ciyar da jiharmu gaba, ina nufin ka ba su aiki.
Mai Girma Gwamna, ina kiranka da ka temaka ka ji kiran talakawan jiharka masu son zaman lafiya da cigaban jiharsu, ka sanar da dawo da tura ‘yan musabaka karo karatu a jawabinka na ranar rufe musabakar bana, wanda za a yi ranar Alhamis, 20 ga Janairu, 2022.
Shawarata
Mai Girma Gwamna, na san za ka amsa kirana kuma kiran makaranta Al-Kur’ani, to idan ka amsa, ga shawarata kan yanda za a kara inganta tsarin.
A cigaba da bayar da dama ga duk mai son karo karatun a kowanne fanni kuma a kasashe masu saukin karatu, kamar yanda a kai a lokacinmu, sannan a kirkiro da tsarin rubuta yarjejjeniyar yin aiki na akalla shekaru biyu ko uku ga duk wanda ya mori tsarin.
Haka kuma, a kirkiro da tsarin kara bayar da dama ga wadanda sukai fice a karatun domin dorawa har sukai matakin PhD.
A samar da kwakkwaran kwamiti kan hakan, na ingantattun mutane masu kishin cigaba, kuma masu alaka da al’amarin.
Kammalawa
A karshe ina godiya da samun lokacinka, Allah Yai maka jagora, Ya ba ka damar cigaba da shuka alkhairi a Jigawa wanda zai zame maka gata duniya da lahira.
Sai mun ganka a ranar Alhamis, 20 ga wannan wata, a wajen rufe musabakar jiha ta bana (2022).
Na Gode!
Kabiru Zubairu,
Birnin Kudu, Jihar Jigawa