Daga: Haruna Shuaibu Danzomo
A matsayi na matashin dan jam’iyyar PDP tun daga kafuwar ta zuwa yau, ina son in yi amfani da wannan dama in bawa kwamatocin da suke da ruwa da tsaki wajen tsara yadda Babban Taron Jam’iyyar PDP (convention) na kasa zai kasance.
Ina nufin Ina son su tsaya tsayin daka don ganin sun fitar da nagartaccen mutum a matsayin Shugaban Jam’iyya na Kasa domin halin da jam’iyyar take cike bata bukatar butulun dan siyasa ya jagorance ta.
Lalle ya kamata a duba mutum mai daraja da yakana da gudun abin duniya da zuhudu irin na siyasa.
Naga mutane rututu sun fito, amma ina son don Allah a lura wasu fa wakilan APC ne a cikin mu, domin a shekarar 2015 da 2019 ma da hadin bakin su aka kayar da mu, wasu kuma ‘yan ina da kudi ne wadanda kafin su samu dama ma aikin su shine hada husuma a cikin jam’iyya don neman na Magi.
Lalle kar a yi la’akari da zaman mutum a cikin jam’iyya ko kuma zare idanun sa, kawai ayi la’akari da wanda yake da kishin jam’iyyar PDP a cikin zuciyar sa.
Hakazalika yana da kyau a dauki mutumin da bashi da abokan gaba masu yawa a cikin jam’iyya domin shine zai iya hada kan mutane cikin kankanin lokaci sabanin wadanda suke da makiya wadanda zasuyi amfani da kujerar wajen kawar da wasu da basa so.
Idan kuma aka yi son zuciya batu na gaskia, ba zamu ga da kyau ba, Hausawa dai na cewa, idan kunne yaji gangan jiki ya tsira.
Haruna Shu’aibu Danzomo
Daga Jihar Jigawa