For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Na Neman Shawarar INEC Kan Zaben ‘Yar Tinke

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rubuta wasika zuwa ga shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, Farfesa Mahmoud Yakubu, inda ya bukaci INEC ta yi tsokaci kan kudirin gyaran dokar zabe da majalisar dokokin kasar ta zartar a ranar 9 ga watan Nuwamba.

Buhari, wanda ya karbi kudirin a ranar 19 ga watan Nuwamba, yana da wa’adi zuwa ranar 19 ga watan Disamba na ya rattaba hannu ko kuma ya bayyana ra’ayinsa game da kudurin dokar.

Idan kuma bayan kwanaki 30, shugaban kasar ya ki sanya hannu a kan kudirin kuma Majalisar Dokokin kasar ba ta goyi bayan gyaran da Shugaban kasa ya yi ba, Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su iya dawo da kudirin su amince da shi.

Idan har an zartar da kudurin da aka aike wa shugaban kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un majalisun biyu, nan take kudurin ya zama doka koda ba tare da sa hannun shugaban kasar ba.

Sai dai wasu manyan majiyoyi sun shaidawa jaridar PUNCH a ranar Litinin din da ta gabata cewa kawo yanzu shugaban bai ga wata matsala a kudirin ba amma yana neman shawara daga INEC da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN).

Wata majiya mai karfi ta INEC ta ce, “Mun samu wasika daga shugaban kasa a makon da ya gabata dangane da matsayar INEC kan gyaran dokar zabe musamman dangane da gudanar da zaben fidda gwani da gwamnoni da dama suke da suka a kai.

“Ya kamata mu ba da amsa cikin kwanaki bakwai. Na san cewa za a aika da sakamakon ga shugaban kasa kowane lokaci daga yanzu.”

Da akai tambayar ko INEC za ta amince da zaben fidda gwanin ta hanyar ‘yan tinke, majiyar ta ce hukumar za ta nuna matsayinta ne kawai a kan cancanta da rashin cancantar kudirin sannan ta bar shugaban kasa ya yanke shawarar.

Wani jami’in hukumar ta INEC ya shaidawa jaridar PUNCH cewa majalisar kasa ba ta tattauna da hukumar kan batun zaben fidda gwani ba sai dai kawai maganar aika sakamakon zabe ta hanyar na’ura da sauran batutuwa.

“A lokacin gyaran dokar zabe mun gana da majalisar dokokin kasar amma ba a taba tattauna batun zaben fidda gwani ba. Mun tattauna batun tura sakamako ta hanyar na’ura, da zaben ‘yan kasashen waje da dai sauran batutuwa. A lokacin da aka amince da rahoton ne aka kara da zaben fidda gwani kai tsaye a cikin kudirin.

“Don haka INEC ba a taba ba ta damar gabatar da matsayin ta ba kan wannan batu. Abin da shugaban kasa ya yi a yanzu shi ne mu sanar da matsayarmu kan lamarin. Gaskiyar ita ce, idan INEC ba za ta iya gudanar da zaben fidda gwanin kai tsaye ba, hakan zai mayar da dokar ta zama marar amfani,” inji shi.

Da aka tuntubi babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce shugaban zai ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan lamarin kafin a rattaba hannu kan kudirin.

A kan wadanda Shugaban kasar zai tuntuba kan kudirin dokar, Garba Shehu ya ce, “Shugaban zai tuntubi wadanda ya ke ganin suna da muhimmanci kan shawararsa da kuma wadanda za su iya ba shi shawara kan dokar zabe. Kuma zai sadu da su. Amma ba zan iya bayyana yanda abun zai kasance ko takamaiman suna ba kuma in ce wannan shine wanda shugaban zai iya saduwa da shi. A karshe ya yanke shawara.”

Kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye, a farkon watannan ya ce yin zaben fidda gwani kai tsaye zai fi tsada sosai saboda dimbin ma’aikatan da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaben.

Okoye ya ce hukumar za ta kuma bukaci kimanin jami’ai biyu da za su sa ido kan zaben a kowace mazaba cikin mazabu 8,809 da ke kasar, wanda ya kai adadin ma’aikata 17,600. Ya kuma shaida wa jaridar PUNCH cewa hukumar za ta bukaci yin amfani da matasa masu hidimar kasa su gudanar da zaben fidda gwanin kai tsaye saboda INEC ba ta da karfin ma’aikata.

Jaridar PUNCH ta kuma ruwaito cewa idan aka yi la’akari da hauhawar farashin kayayyaki, farashin canjin kudi da kuma bukatar sayen karin kayan aiki sakamakon kone-konen ofisoshin INEC musamman a yankin Kudu-maso-Gabas, zaben shekarar 2023 na iya cin sama da Naira Biliyan 350.

Comments
Loading...