For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Ba Ya Goyon Bayan Cire Tallafin Mai – Ministan Mai

Karamin Ministan Ilimi, Timipre Sylva ya bayyana hakan ne a tattaunwarsa da Channels Television a ranar 24 ga Janairu, 2022.

Ministan ya ce, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ya goyon bayan cire tallafin man fetur.

Ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta shirya kammala tuntuba kafin ta fito da tsarin da za a bi karara a kan batun.

“Zan fada maka karara cewa, a halin yanzu, cire gabaki dayan tallafin mai ba ya cikin tsarinmu,” inji Sylva.

“Shugaban Kasar Najeriya ba ya goyon bayan cire tallafin mai a wannan lokaci,” in ji shi.

A dai watan Nuwamban da ya gabata ne Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed, ta sanar da cewa Najeriya za ta cire tallafin mai a watan Yuni na 2022 tare da maye gurbinsa da tallafin naira 5000 a wata ga ‘yan Najeriya masu fama da matsanancin talauci a matsayin tallafin sufuri.

KU KARANTA: Cire Tallafin Mai Zai Kara Jefa Talakawa Cikin Mawuyacin Hali – Abdussalami

Ana tsaka da cece-kuce kan lamarin ne dai, Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan, a Talatar da ta gabata ya bayyana cewa, Shugaba Buhari bai bayar da umarnin cire tallafin mai ba.

Sylva ya bayyana cewa, matsayin Shugaban Kasa kan kalubalantar cire tallafin shine, yana kallon irin takurin da hakan zai jawo ‘yan-kasa.

Ya kuma bayyana wasu daga cikin zabin da hukumomi ke dubawa game da al’amarin.

“Muna aiki kan batun,” in ji ministan. “Tabbas mun san cewa abu ne da ya kamata. Tabbas mun san da cewa zai zama yana da takura a kan mutane, shine ma yasa muke duba wadannan abubuwa.

“Har sai an daidaita wadannan abubuwa tare da kungiyar kwadago, da kuma duk masu ruwa da tsaki a bangaren, ba za mu cire tallafin ba. A yanzu haka, ba ya cikin abun da ke gabanmu, ina tabbatar maka da haka.

“Wannan wani abu ne da ya kamata a duba shi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma jihohi, saboda wannan abu ne da ya shafi kasa gaba daya. Muna aiki tare da gwamnoni domin mu gano yanda za mu gudanar da tsarin na tallafin mai saboda kyakkywar gobe.”

Comments
Loading...