For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Dokar Zabe

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fuskantar matsin lamba kan ya yi watsi da kudirin gyaran dokar zabe na shekarar 2022.

Majiyoyi sun baiyana cewa, wadanda ke takurawa Shugaba Buhari kan yin watsi da kudirin dokar suna kafa hujja ne da wadansu sassa da suka kira da na ‘dakushe demokaradiyya’.

Sai dai kuma, idan har an sanyawa dokar hannu, jam’iyyun siyasa za su gabatar da sunayen ‘yan takarar shugaban kasa a ranar 18 ga watan Agusta mai zuwa, kimanin watanni 6 kafin babban zaben shekarar 2023.

Jadawalin zaben shekarar 2023 na Hukumar Zabe ya nuna cewa, za a yi zaben shugaban kasa ne a ranar 18 ga watan Fabarairu na shekarar 2023.

Duba da kudirin dokar zabe da akaiwa kwaskwarima, za a mika sunayen ‘yan takara, a yi zaben fidda gwani na ‘yan takarar shugaban kasa, gwamna, ‘yan majalissun jiha da na tarayya a tsakanin watan Yuli da tsakiyar watan Agusta.

Wata majiya ta ce, “Shugaban Kasa zai iya kin sanya hannu a dokar saboda ‘abubuwan da suke nuni da dakushe demokaradiyya’ a gyaran kudirin dokar zaben na shekarar 2022.

“Akwai yiwuwar za ai amfani da dokar zabe ta shekarar 2010 (wadda akaiwa kwaskwarima) a zaben shekarar 2023 saboda bakin tanade-tanade.

“Alal misali, bai dace da doka ba a cire masu rike da mukaman siyasa daga shiga zaben fidda gwani. Abin ya nuna ministoci, kwamishinoni, da sauransu ba za su shiga zabe ba.

“Haka kuma, kasar ba ta da karfin iya amfani da na’ura wajen yin zabe da na’ura. Mafi yawan ‘yan siyasa a jam’iyyar APC da PDP ba su gamsu da hakan ba.”

Ya kara da cewa, “Sashin yin sasanto wani abu ne na rudani, kuma kokari ne na kalubalantar gwamnonin da suke son kakaba ‘yan takara. Saboda haka, zamu yi tsammani Shugaban Kasa zai yi watsi da kudirin.”

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN ya ce, ya karbi gyararren kudirin dokar zaben da Shugaban Kasa ya aike masa a ranar Litinin domin ya bayar da shawara.

Malami ya ce, zai baiwa Shugaban Kasa shawarar ya sanya hannu idan har kudirin ya dace da abin da ‘yan kasa ke so.

Wasu tanade-tanaden da ke cikin kudirin sun nuna cewa, hukumar zabe za ta iya amfani da na’ura wajen yin zabe.

Wasu tanade-tanaden a cikin kudirin an hana ministoci, kwamishinoni, da sauran masu rike da mukaman siyasa kasancewa wakilan jam’iyya a wajen kada kuri’a.

Haka kuma, babu wani mai rike da mukamin siyasa a kowanne mataki, minista ne ko kwamishina ko mamba na board da zai yi zabe ko a zabe shi a zabukan fidda gwani.

Comments
Loading...