For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Na Ganawar Sirri Da Shugabannin Tsaron Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na ganarwar sirri da shugabannin tsaron Najeriya a fadarsa da ke a Abuja.

Ganawar wadda aka fara da misalin karfe 10 na safiyar Alhamis din nan, ta samu halartar Mataimakin Shugaba Kasa, Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Bashir Magashi da Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama.

Comments
Loading...