Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bayar da sabon tallafin bashi ga jihohi 36 na Najeriya mai yawan Naira Biliyan 656.112.
Wannan ya fito ne ranar Alhamis a taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, a sanarwar da ya fitar bayan taron, ya bayyana cewa kowacce jiha za ta sami Naira Biliyan 18.225 a kan kudin ruwa kashi 9 cikin 100.
Jihohin za su biya bashin ne cikin shekaru 30 bayan shekaru 2 na shirye-shiryen biyan.
Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa, an dau wannan mataki ne domin temakawa jihohin wajen magance matsalolin kudade.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta sanar da Majalissar ce, yanzu haka Babban Banki Najeriya na shirya tallafin.
Za a bayar da tallafin bashin Naira Biliyan 656.112 ga jihohin ne cikin kashi shida a watanni shida.
Zainab Ahmed ta kuma bayyanawa Majalissar cewa, za a fara cire kudade daga asusun jihohi domin biyan tallafin bashin baya da aka baiwa jihohin daga Babban Bankin.
Labari: Kabiru Zubairu