Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce malamai za su fara more sabon tsarin albashin da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi alkawari, daga watan Janairun shekarar 2022.
Nwajiuba ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wani taron karawa juna sani da ma’aikatar ilimi ta shirya wanda jaridar PUNCH ta halarta.
Jaridar ta rawaito cewa, taron karawa juna sanin wani bangare ne na ayyukan bikin ranar Malamai ta Duniya mai zuwa ta shekarar 2021 tare da taken, ‘Malamai a Matsayin Tushen Farfado da Ilimi’.
Ministan, wanda babban sakataren ma’aikatar, Sonny Echono ya wakilta, ya bayyana cewa ana aikin kammala ingantaccen tsarin albashin ga malaman.
Ya kuma bayyana cewa ana kuma aiki a kan wasu abubuwan karfafa gwiwa ga malaman da Shugaban ya yi alkawari a lokacin Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2020.
Ya jaddada cewa sauran abubuwan da aka tanada domin kara masu kwarin gwiwa sun hada da alawus-alawus, gidaje, horo, da kuma tsawaita shekarun kafin ritaya daga 35 zuwa 40.
Echono ya ce, “Shugaban kasa ya amince da ingantaccen tsarin albashi kuma za mu kammala shi ba da jimawa ba. Shugaban ya amince da cewa yakamata ya fara aiki daga shekarar 2022.
“Muna yin duk abin da za mu yi don tabbatar da cewa kafin Janairun 2022, yakamata malamai su sami albashin da suka cancanci samu. Muna bin diddigin tsarin aiwatarwar cikin sauri don ganin cewa a karshen shekara, za mu iya gaya wa Shugaban kasa cewa duk abubuwan karfafawa da ya amince da su a shirye suke don fara aiwatarwa.”
Ya yabi shugaban kasar bisa wannan kokari na farfado da kimar malamai da kuma tsarin koyarwa a Najeriya.
“Abin da kawai ake bukata shi ne ga sauran masu aiwatar da ayyukan kasa kamar gwamnonin jihohi, Majalisar kasa da sauran su su shiga cikin wannan yunkurin tare da tabbatar da cewa an aiwatarwar da shi ba ta da matsala.”