For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Ya Baiyana Hanya Da Nagarta Da Za A Duba Wajen Fitar Dan Takarar APC Na Shugaban Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau Talata ya baiyana hanyar zabar dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC domin tunkarar zaben shekarar 2023.

Shugaban Kasar ya baiyana hakan ne lokacin da yake ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC a Abuja.

“Dole ne manufarmu ta zama samun nasarar jam’iyyarmu kuma zabinmu dole ne ya zama kan wanda zai samawa talakawan Najeriya nasara tare da ba su kwarin guiwa tun ma kafin lokacin zabe,” in ji Shugaba Buhari, kamar yanda mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya rubuta a sanarwar bayan zaman.

Jam’iyyar APC dai ta fara tantance ‘yan takararta na shugabancin kasa a jiya Litinin, kuma ana sa ran zata gudanar da zaben fidda gwani na masu neman takarar a ranakun 6, 7 da 8 ga watan Yuni mai kamawa, inda zata fitar da dan takara daya daga cikin masu neman takarar su 23.

A lokacin zaman na yau Talata tare gwamnonin, Shugaban Kasar ya bukaci su da tabbatar da cewa jam’iyyar ta zabi dan takarar da ya dace da manufofin jam’iyyar APC.

“Shirye-shiryen babban zaben shekarar 2023 ya fara, kuma na gano cewa, jam’iyyun da suke samun nasara a duniya suna dogara ne da daidaiton cikin gidansu da kuma kakkarfan jagoranci domin su cimma babban rabon siyasa,” in ji shi.

“Jam’iyyarmu, APC, bai kamata ta zama ta daban ba, dadin dadawa, har yanzu muna aiwatar da manufofinmu na samar da ingantacciyar kasa.

“Kamar yanda na fara shekarata ta karshe a karo na biyu a matsayin Shugaban Kasa kuma jagoran jam’iyyarmu, na gano bukatar da ke kaina ta na samar da kakkarfan shugabanci ga jam’iyya a lokacin nan na sauya mulki kuma na tabbatar da cewa abun ya faru cikin yanayin da ya dace.

“Ana bukatar irin wannan jagoranci domin jam’iyya ta ci gaba da kasancewa mai tasiri kuma dunkulalliya. Haka kuma mu kara damar samun nasarar siyasarmu ta hanyar tabbatar da cewa mun rike mulkin kasa, da mafi yawancin ‘yan majalissu, mu kuma sami karin jihohi.

“A ‘yan kwanaki masu zuwa, jam’iyya zata gudanar da babban taro domin fitar da wanda zai daga tuta jam’iyyar a zaben shekarar 2023 a matsayin dan takarar shugaban kasa. Wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci kuma sakamakonsa zai tabbatarwa duniya irin kyakkyawan kudiri da jam’iyyar APC ke da shi ga tsari, al’ada, da kuma mulkin demokaradiyya.

Shugaban Kasar ya kuma roki gwamnonin “da ku bar ra’ayinmu ya ci gaba, himmarmu ta ci gaba da kasancewa a tsarin samar da canji a al’ummarmu da fatan ‘yan kasa da sauran mutanen duniya”.

Da yake jawabi a madadin gwamnonin, Shugaban Kungiyar Gwamonin APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya ce, dole ne jam’iyya ta dora a kan nasarorin da ta samu a lokacin zaben shugabanninta, da zabukan fidda gwanin da aka gudanar kawo yanzu, sannan ta fito da dan takara wanda zai nuna kishi da son kasa, wanda Shugaban Kasa ya nuna.

“Zamu goyi bayan Shugaban Kasa wajen samun ingantaccen zaben fidda gwani na dan takarar Shugaban Kasa,” in Gwamna Atiku Bagudu.

Comments
Loading...