Akwai yiwuwar Shugaban Kasa Muhammadu ya bayar da sunayen mutane biyu da suka hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da kuma Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan a matsayin wadanda yake so su gaje shi.
A baya dai an rawaito cewa, Shugaban Kasa Buhari, ya roki gwamonin jam’iyyar APC da su kyale shi ya zabi wanda yake so a matsayin magajinsa a lokacin zaben fitar da gwani wanda za a gudanar ranar 6 ga watan Yunin da muke ciki.
Shugaba Buhari ya yi kiran ne lokacin ganawa da gwamnonin da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Talatar da ta gabata.
Wata majiya daga fadar Shugaban Kasa ta ce, Buhari na cikin tsaka mai wuya a wajen zabi tsakanin Ahmad Lawan da Osinbajo, biyo bayan baiyanar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar a matsayin mai yi wa jam’iyyar PDP takara.
Jaridar DAILY SUN ta gano cewa, akwai rukunin mutanen da aka ware suna duba alfanu da kuma matsalolin da ke tattare da Ahmad lawan da kuma Yemi Osinbajo domin su baiwa Shugaba Buhari shawara kan hukunci na karshe da ya kamata ya yanke bayan ya dawo gida a ranar Juma’ar gobe.