For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari ya Bukaci Majalissar Tarayya Ta karfafa Tsarin Dimokradiyyar Najeriya

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya wakilci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a taron ‘yan majalissar tarayya na shekarar 2021 a Abuja, ranar 13 ga Disamba, 2021.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta tabbatar da abubuwan da za su karfafa dimokradiyyar kasar.

Da yake jawabi a wajen taron na shekarar 2021 da Majalissar hadin gwiwa da Cibiyar Nazarin Dokoki da Dimokaradiyya ta Kasa (NILDS), suka shirya, ya ce bangaren zartarwa zai ci gaba da hada gwiwa da Majalisar Dokokin ta kasa.

A cewar shugaban, akwai bukatar hakanne domin gudanar da sahihin mulki da kuma aiwatar da kudirin doka don amfanin ‘yan Najeriya baki daya.

Ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun yi kira da a sake duba kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, shugaban kasar ya kuma ce yana sane da cewa majalisar dokokin kasar na jan hankalin masu ruwa da tsaki a harkar gyaran kundin tsarin mulkin kasar.

“Hakazalika, ina kalubalantarku da ku tabbatar da cewa wannan jerin lakcoci ya dore kuma a yi niyya don magance muhimman al’amuran ƙasa da na tsarin mulki ta hanyar da za ta ƙarfafa dimokuradiyyarmu, kawar da matsaloli da kuma tabbatar da kyawawan ayyuka,” in ji Shugaba Buhari.

“Bangaren zartarwar gwamnati zai ci gaba da gina kyakkyawar alakar aiki da ake da ita da majalisar dokoki domin tabbatar da ganin an ci gaba don amfanin kowanne dan Najeriya.

“Saboda haka, ina ba da kalubalantar Majalisar Dokoki ta kasa da Cibiyar Nazarin Majalisu da Dimokuradiyya da su tabbatar da cewa sakamakon ya kasance abin da za a adana.”

Comments
Loading...