For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Ya Ce Ba Ya Tsammanin Yabo Daga ‘Yan Najeriya

ShugabaMuhammadu Buhari ya ce ba ya tsammanin yabo daga ‘yan Najeriya bayan kare wa’adin mulkinsa.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da NTA a ranar Alhamis.

Buhari ya ce cikin shekarun da ya yi a kan mulki ya yi abubuwa da dama a Najeriya, kuma ya yi duk abin da zai iya ga Najeriya inda ya kara da cewa “me kuma zan iya kara yi wa wannan kasar?”

KU KARANTA: Ina Sane Da Irin Wahalar Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki – Buhari

Ya kuma ce yana fatan lokacin da wa’adinsa zai kare a shekarar 2023, ‘yan kasar za su gano cewa ya yi wa kasar kokari iya iyawarsa.

“Na yi gwamna, na yi minista yanzu kuma ina shugaban kasa a karo na biyu. Don haka na taka duk wani matsayi na gwamnati, me kuma zan yi wa wannan kasar?” in ji Buhari.

“Na yi iya kokari na, ina kuma fatan bayan na bar shugabanci, ‘yan Najeriya za su fahimci abun da na yi. Bana tsammanin wata godiya amma ina sa ran ‘yan Najeriya za su ce wannan mutumin ya yi mana kokari. wannan nake tsammani daga ‘yan Najeriya.”

Daga: BBC Hausa

Comments
Loading...