Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a jiya Litinin ya shiga cikin Musulmi a Masallacin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja wajen halartar buɗe tafsirin Alkur’ani na watan Ramadhan na bana.
A bayanin da Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Garba Shehu ya sanyawa hannu, Buhari ya shiga cikin addu’ar fatan samawa Najeriya zaman lafiya, cigaba da kuma samun walwalar dukkanin al’umma.
Babban limamin masallacin, Sheikh Abdulwahab Sulaiman, wanda ya jagoranci tafsirin, ya kushe ƴan ta’adda wadanda ke amfani da Musulunci a matsayin madogara wajen yin sata da kashe mutane.
Shugaba Buhari ya jaddada bukatar yafewa juna, tausayi da kuma kyautatawa mabukata.
Ya yi addu’ar Allah Ya kawo karshen aiyukan ƴan ta’adda, ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma annobar Covid-19 da sauran matsalolin da ke addabar Najeriya da sauran duniya.
(PUNCH)