Shugaba Muhammadu Buhari ya je ziyarar ta’aziyya wajen iyalan Marigayi Cif Ernest Shonekan, Tsohon Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya a Najeriya.

Buhari, ya ziyarci iyalan marigayin ne a gidansu da ke birnin Lagos a daidai lokacin da ya je jihar Ogun kaddamar da wasu aiyuka.
KU KARANTA: Dr. Ahmad Ibrahim BUK, Kala Haddasana Ya Rasu
Cif Ernest Shonekan dai ya rasu ne ranar Talata, 11 ga wannan wata na Janairu, a Lagos bayan gajeriyar jinya, ana dan shekara 85.
Rahotanni sun nuna cewa, kafin ziyarar Buhari, jami’an tsaro sun tsaurara tsaro a zagiyar gidan tsohon shugaban Cif Ernest Shonekan.