Tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya caccaki jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya bisa gazawa wajen yiwa ƙasar abin da ya kamata a tsawon shekaru 7 na mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Saraki ya yi wannan caccakar ne a lokacin da yake yiwa wakilai (delegates) na jam’iyyar PDP jawabi a yayin ziyararsa birnin Ibadan a jiya Talata.
Ya baiyana cewa, Najeriya tana da rauni lokacin da Buhari ya karɓi shugabancinta, amma a yanzu haka Buharin ya wargaza ƙasar inda ta zama ƙasar da ta gaza.
Sanata Bukola Saraki dai daya ne daga cikin ƴan jam’iyyar PDP da ke neman damar shugabantar Najeriya a shekarar 2023.
Ya baiyana cewa, ya shirya domin magance matsalolin Najeriya, inda ya ƙara da cewa, a wannan yanayi, Najeriya na buƙatar ƙwararren shugaba wanda zai jagorance ta wajen ficewa daga halin ƙuncin da take ciki.
Saraki ya ce, yana da duk abin da ake buƙata wajen ganin an cimma nasarar da ake buƙata a ƙoƙarin dawo da Najeriya cikin haiyacinta.
Ya ƙara da cewa, Najeriya na buƙatar shugaban da zai haɗa kan ƴan Najeriya, inda ya ce rarrabuwar kan da aka haifar ta hanyar ƙabilanci, addinai da sauran halayen son zuciya sun dabaibaye ci gaban ƙasar.
Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Oyo, Dayo Ogungbenro; Sakataren Jam’iyyar PDP na jihar, Wasiu Adeleke; tsohon Ministan Wutar Lantarki, Dr Wole Oyelese; mamba a Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Dr Saka Balogun; da kuma Mrs Bose Adedibu, wadda ita ce Shugabar Mata ta PDP a jihar suna kan gaba cikin wadanda suka karɓi Sanata Bukola Saraki.
A lokacin ziyarar, Saraki ya kuma ziyarci Gwamnan Jihar, Seyi Makinde, wanda ya baiyana cewa, jam’iyyar PDP za ta fitar da ɗan-takarar da zai ci zaɓe kuma ya kuɓutar da Najeriya daga halin ƙuncin da take ciki.
Ya ƙara da cewa, ƙasar ta fuskanci ƙalubale da dama ƙarƙashin jagorancin APC, wanda hakan ya jawo ƴan Najeriya suka yi watsi da ita, inda ya ce tabbas akwai buƙatar samun ya-kamata a tsarin gwamnati.