Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai damu da wanda zai gaje shi ba a matsayin shugaban kasa saboda “na ajiye bayanan komai da komai”, in ji shi.
Shugaban ya faɗi hakan ne a hirarsa da tashar talabijin ta Channels a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa “zaben 2023 ba matsalata ba ce”.
“Ban damu da wanda zai gaje ni ba, rabu da shi ya zo ko ma wane ne,” in ji shi.
KU KARANTA:
- Zan Amince Da Gyaran Dokar Zabe Idan Majalissa Ta Bayar Da Zabi Wajen Zaben Fidda Gwani – Buhari
- Kungiyar CAN Ta Yi Barazanar Daukar Mataki Idan A Kai ‘Yan Takara Musulmi A Najeriya
- Iya Iyawar Buhari Kenan, Ba Zai Iya Kara Komai Ba – Obasanjo
Da yake amsa tambaya kan ko me ke zuwa masa a rai idan ya ji an ambaci zaben 2023, Buhari ya amsa da cewa: “Ba matsalata ba ce.”
Da aka tambaye shi: “Ba ka damu game da wanda zai gaje ka ba? Sai ya ce:
“Bar shi ya zo ko ma wane ne. Na tabbata na ajiye bayanan duk wani abu mai muhimmanci. Bai kamata wani ya kira ni da shaida a gaban kotu ba a kan wani abu, idan ba haka ba kuma zai shiga matsala.”
Buhari ya kuma boye sunan wanda yake so ya gaje shi saboda ya tseratar da shi daga masu kalubalantarsa.
“A’a, saboda idan na fada za a iya kawar da shi. Gara na bar shi a sirrance,” a cewarsa.