For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Ya Nada Atterwahmie Shugabancin FMC Birnin Kudu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie a matsayin shugaban asibitin gwamnatin tarayya, FMC, Birnin Kudu.

Nadin Atterwahmie ya fara aiki daga ranar 23 ga watan Nuwamba na shekarar 2021 kuma zai kwashe shekaru 4 a kan wannan mukami.

Shugaban kasar ya kuma yi kira ga sabon shugaban asibitin da ya dora daga inda wadanda ya gada suka tsaya wajen kokarin inganta asibitin.

Takardar nadin sabon shugaban asibitin da Karamin Ministan Lafiya, Dr. Adeleke Mamora ya sanyawa hannu, ta yi kira ga sabon shugaban da ya dage wajen tabbatar da manufofin gwamnatin shugaba Buhari na inganta al’amura.

Kafin nadinsa, Atterwahmie, babban likita ne a bangaren haihuwa na asibitin gwamnatin tarayya da Nguru, jihar Yobe.

Comments
Loading...