For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Ya Nada Sani Zorro A Matsayin Mataimaki Na Musamman Ga Aisha Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau Asabar ya amince da nadin tsohon dan Majalissar Tarayyar, Muhammad Sani Zorro a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Matar Shugaban Kasa kan Al’amuran Al’umma da Tsare-tsare.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Kasar ya amince da canjin wajen aiki ga wasu masu temakawa matar tasa su su 3 zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Mai Bayar da Shawara na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai, Femi Adesina ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Femi Adesina ya ce, wadanda aka dauke daga Ofishin Matar Shugaban Kasar sun hada da: Dr. Mohammed Abdulrahman, wanda kafin dauke shi shine Babban Mai Temakawa kan Harkokin Cigaban Lafiya, kuma Likitan Matar Shugaban Kasa; Hadi Uba, wanda da shine Mai Temakawa a Bangaren Shugabanci; da kuma Wole Aboderin, wanda shi kuma a da shine Mai Temakawa kan Hulda da Hukumomi masu Zaman Kansu.

Haka kuma sanarwar ta Adesina ta nuna cewa, Shugaban Kasa Buhari ya amince da korar Zainab Kazeem wadda a da ita ce Mai Temakawa ta Musamman kan Harkokin Cikin Gida a Ofishin Matar Shugaban Kasa.

Sabon Babban Mai Temakawa na Musamman a Ofishin Matar Shugaban Kasa, Muhammad Sani Zorro dai kwararren dan jarida ne kuma jagora a aikin jarida a Najeriya, Afirka da ma Duniya.

Ya shugabanci Kungiyar ‘Yanjarida ta Najeriya a lokuta da dama, yayinda kuma ya taba zama Shugaban Kungiyar ‘Yanjarida ta yankin Afirka ta Yamma da kuma Shugaban Kungiyar ‘Yanjarida ta Nahiyar Afirka gaba daya.

Ya taba zama dan Majalissar Wakilai, inda ya shugabanci kwamitin kula da al’amuran ‘yan gudun hijira a yankin Arewa maso Gabas.

Comments
Loading...