Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau Juma’a ya rantsar da Alhaji Muazu Sambo a matsayin Karamin Ministan Aiyuka da Gidaje.
Sambo ya karbi rantsuwar ne a gaban shugaban kasa a farfajiyar Majalissar Zartarwa da ke fadar shugaban kasa a Abuja.
A yanzu haka Sambo shine wakilin jihar Taraba a Majalissar Zartarwa ta Najeriya tun baya tube Saleh Mamman da shugaba Buhari yai a kwanakin baya.
Sabon ministan wanda Injiniyan Gine-gine ne, a farkon satin nan ne Majalissar Dattawa ta tantance shi bayan ta karbi sunansa daga shugaban kasa a makon da ya gabata.