For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Ya Roki ‘Yan Jaridu Su Dena Cewa Tsaro Ya Tarbarbare

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya hori kafafen yada labarai da su kula kan yanayin yanda suke bayar rahotonnin tsaro da na samar da zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa da Babban Mai Temakawa Shugaban kan Kafafen Yada Labarai, Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu ya kuma fitar a Litinin din nan, ya ce cewa ‘tabarbarewar tsaro’ ya kamata a yi masa madadi da ‘gaskiyar raguwar matsalolin tsaro’.

Sanarwar, an mata take da ‘Shugaba Buhari na Taya Musulmi Murnar Mauludi’ wadda a cikinta shugaban ya tabbatar da cigaban da ake samu wajen magance matsalolin tsaro.

A cikin sanarwar an rubuta cewa, “Shugaban Kasa na kira ga Musulmi da su dage wajen yin yafiya da son juna kamar yanda yake a rayuwa da koyarwar Manzon Allah (SAW) wanda ake murnar zagayowar ranar haihuwarsa a wannan rana mai girma. A wannan lokaci mai muhimmanci, ina yiwa kowa fatan samun alkhairan wannan rana.

“Shugaban ya yi amfani da wannan damar wajen sanar da irin cigaban da ake samu a aiyukan sojoji, ‘yan sanda, da jami’an farin kaya wajen magance matsalar tsaro kasa.

“Ya ce, gwamnatin ta shirya tsaf kuma tana fatan wannan nasara ta cigaba, yayin da yai kira ga kafafen yada labarai da su kula da yanayin kalamansu da sanya kwarewa wajen harkokin tsaro da samar da zaman lafiya. Lokaci ya yi da za amusanya kalaman “tabarbarewar tsaro” da “cigaban da ake samu wajen samar da tsaro”.

“Shugaban Kasar ya kara da cewa karuwar samun hadin kai daga ‘yan kasa da jajircewar ‘yan sanda da sauran jagororin tsaro na temakawa wajen samun nasarorin da ake samu akan ta’addanci, tashe-tashen hankula da yiwa tattalin arziki zagon kasa. Gaskiyar nasarar da ake samu wajen magance matsalar tsaro ya kamata ta maye gurbin maganganun cewa ana samun tabarbarewar tsaro a kasar”.

Garba Shehu ya rawaito Shugaba Buhari nacewa, “Baya da aiyukanmu da muke yi, jami’an tsaronmu da ke ba da gudunmawa wajen samun nasarar da ake samu na bukatar samun goyon bayanmu da kuma bas u karfin guiwa domin su kara dagewa. Dukkan ‘yan kasa da kuma tsarin yada labarai na da nauyi a kan hakan.

A karshe, Shugaba Buhari ya roki masu amfani da tituna da su yi tuki da kulawa su kuma kaucewa fadawa hatsari.

Comments
Loading...