Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa Kudirin Dokar Zabe ta shekarar 2022 hannu, inda a yanzu ta zama cikakkiyar doka.
Shugaba Buharin ya sanyawa kudirin dokar hannu ne yau Juma’a a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
A lokacin sanya hannu a kudirin dokar, Shugaban yana tare da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila, wadanda duk suka shaida sanya hannu.

Sai dai kuma a jawabin da Shugaba Buhari ya gabatar kafin sanya hannun ya ce, akwai bukatar Majalissar Tarayya ta koma ta goge sashi na 84(12) wanda ya hana masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara ko yin zaben fidda gwani har sai bayan sun ajjiye mukamansu kwanaki 30 kafin zaben fidda gwani.