For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Ya Hori Shugabannin Duniya Kan Biyayya Ga Tsarin Mulki

Daga: Kabiru Zubairu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa shugabannin duniya a ranar Juma’a a birnin New York cewa, halin da ake ciki na kwacen mulki ba bisa ka’ida ba, don nuna kiyayya ga sauye -sauyen tsarin mulki da wasu shugabanni ke yi, bai kamata kasashen duniya su yarda da shi ba.

A cikin jawabinsa a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na 76, Shugaban ya yi gargadin cewa nasarorin dimokradiyya na shekarun da suka gabata a Yammacin Afirka ” yanzu ana lalata su ” saboda irin wadannan munanan halaye.

Ya tabbatar da goyon bayan Najeriya ga kokarin kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), Kungiyar Hadin Kan Nahiyar Afirka (AU) da Majalisar Dinkin Duniya don magance wannan kalubalen da ke ci gaba.

Shugaban y ace; “A matsayinmu na shuwagabannin kasashe akwai bukatar mu yi aiki da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasashen mu, musamman kan wa’adin mulki.”

Shugaban ya bayyana lamarin a matsayin abin da yake ciwa nahiyar Afirka tuwo a kwarya, in da ya bukaci kasashen duniya ba kawai su magance rikice -rikice ba, a a har ma da abubuwan da ke haifar da rikice-rikicen da farko.

“Wadannan sun hada da rashin shugabanci mai kyau da rashin bin tsarin dimokradiyya, da take hakkin dan adam, da talauci, da jahilci, da rashin adalci da kuma rashin samar da daidaito.

“Babu mafita mai sauki ga wadannan yanayi. Akwai bukatar yin kokari na dogon lokaci da samar da ingantaccen hadin gwiwar kasashen duniya.”

Shugaban ya kuma jaddada bukar samun hadin kan kasashen duniya wajen magance rikice-rikice da sauran abubuwan da ke dakushe cigaban duniya.

Ya ce “wannan zai saukaka samun nasarar cimma muradun samun ci gaba mai dorewa na 2030 da Muradin Tarayyar Afirka na 2063. ”

Jawabin Shugaban, wanda ya gabatar a dandalin babban zauren Majalisar, ya yi magana kan wasu batutuwan da suka shafi duniya da ke da alaka da Najeriya, irin su cutar ta COVID-19, Yarjejeniyar Cinikin Makamai, sauyin yanayi, ta’addanci, yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.

Comments
Loading...