Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai hukunta duk wadanda suka shigo da ma’aikata cikin aikin gwamnati ba bisa ka’ida ba ko kuma suka yi aringizon albashi da kuma masu ma’aikatan bogi.
Ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja lokacin da yake bude taron wayar da kai kan magance cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikata karo na uku wanda akaiwa take da ‘Cin Hanci da Tsadar Gudanar da Gwamnati: Sabbin Tsare-Tsare Domin Aiwatar da Gaskiya a Kashe Kudade.
Shugaban ya kuma yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za tai kasa a guiwa ba wajen hukunta shugabannin ma’aikatun da suka kirkiro da sabbin aiyuka don son zuciya alhalin akwai aiyukan da ba a kammala ba a kasafin kudi.
Shugaban ya ce, “Mun rage kashe kudade wajen gudanar da gwamnati ta hanyar cika alkawuran da mukai na kammala aiyukan gwamnatocin baya da akai watsi da su ko kuma ake gudanarwa. Kuma muna tabbatar da cewa hukumomi ba su kawo wasu sabbin aiyuka ba alhalin akwai aiyukan da ake kan gudanarwa.
Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta gano daga aiyukan Hukumar Da’ar Ma’aikata, ICPC, cewa akwai wasu ma’aikatun gwamnati da suke kirkiro sabbin aiyuka baya da akwai aiyukan da ba a kammala ba.
Ya jaddada cewa, “za a cigaba da daukar matakan kora kan duk shugabannin ma’aikatun da aka kama da wannan dabi’a. Ina da tabbacin cewa, ICPC za ta ci gaba da kulawar da ta kamata kamar yanda yake a dokokinta kan wannan matsala.”