Shugaba Muhammadi Buhari zai gabatar da kasafin kudi na shekarar 2022 a ranar Alhamis 7 ga Oktoban 2021.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Ovie Omo Agege lokacin da yake jagorantar zaman majalissar na Talatar nan.
Omo Agege ya bukaci ‘yan kwamitin kudi na majalisar da su dubu takardar tsare-tsaren kashe kudade wadda shugaban ya aikowa majalissar a Talatar nan domin gabatar da sakamako ranar Laraba.